Idonmu Idon Tinubu, Sai Mun Lakaɗa Masa Dukan Kawo Wuƙa -Ƴan Kasuwa Mata Na Najeriya


Wasu ƴan kasuwa mata a jihar Ogun sun yi kira ga Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Tinubu, da ya yi murabus sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da kuma wahalar rayuwa da ake ciki.
Ƴan kasuwar sun yi Allah waidai da gwamnatin Tinubu, tare da yin barazanar lakaɗa masa mugun duka matuƙar suka yi ido biyu da shi.
Mata ƴan kasuwar sun bayyana hakan yayin da suke tattaunawa da wani mai harhaɗa rahoto a cikin wani bidiyo da Sahara Reporters ta gani a ranar Laraba. Sun bayyana cewa Tinubu ya bai wa ƴan Najeriya kunya, musamman ma Yarabawa. Shafin sauraniya news na wallafa a shainsu.
https://www.facebook.com/share/p/54Gxdb1cs7oi5VF8/?mibextid=oFDknk
Wata dattijuwa ta ce, “Ya bai wa Yarabawa kunya. Sam ba ya abu kamar Bayarabe.”
Wata kuma ta ce, “Komai ya yi matuƙar tsada. Har ta ya kai ba ma iya sayen kwano ɗaya na gari. Mun gaji da komai. Lokacin da na fara kasuwanci, katan ɗin kifi naira 200 ne amma yanzu naira 20, 000.
“Ba mu da abincin da za mu ci. Tsofaffi na ta mutuwa. Kasuwanci ba ya tafiya, kuma babu komai a ciki. Kowa yunwa yake ji.
“Wannan matsalar ta yi yawa. Idan ba za ka magance mana matsalarmu ba, kar ka ƙara mana wata.”
Wata ƴar kasuwar kuma ta roƙi shugaban ƙasar da ya ji ƙan ƴan Najeriya, inda ta ce “Mun gaji da Najeriya. Komai ya yi tsada. Komai ƙara tsada yake a kullum.”
“Abin da ya yi mana alƙawari ba shi ke faruwa a yanzu ba. Abin nan ya yi yawa.”
Da aka tambaye su a kan me za su faɗa wa shugaban ƙasar idan suka samu damar haɗuwa da shi, ɗaya daga cikin ƴan kasuwan sai ta ce, “Za mu zane shugaban ƙasar idan muka samu damar haɗuwa da shi. Za mu zane shi. Abin da ya faɗa mana ba shi yake aikatawa ba.”