Hisbah zata gurfanar da murja kunya a gaban kotu
Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhumen yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta gurfanar da fitacciyar ’yar TikTok Murja Ibrahim Kunya a gaban kotu.
Shugaban Hukumar Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar wa TRT Afrika Hausa cewa za a gurfanar da ita ne kan tuhume-tuhumen yin bidiyon rashin tarbiyya a kafafen sada zumunta.
Murja ta shahara musamman a shafukan sada zumunta inda take da miliyoyin mabiya, inda ake ganin tana yawan jawo ce-ce-ku-ce.
A shekarar 2023 ne wata kotu a Kano ta taɓa tura Murja da wasu yan TikTok zuwa gidan gyaran hali.
Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta Hisbah gayyaci Murja domin ja mata kunne.
Haka ma a kwanakin baya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce zai saka ta cikin jerin waɗanda za a yi wa auren zawarawa a Kano.