Hauhawar Farashin Kaya mafi muni da ya addabi Kasar Zimbabuwe
A shekarar 1980 ƙasar Zimbabuwe ta sami ƴancin kai daga hannun Birtaniya. A lokacin sai kana da dalar amurka $1.6 kafin ka sami kuɗin Zimbabwe Zimdollar Z$1. Sannu a hankali darajar kuɗin na Zimbabuwe na ƙara yin ƙasa, har ta kai a shekarar 2008 sai ka sami Z$1000 kafin ka sami dalar Amurka $1. Ka fara mamaki ko? To yanzu za ka ji babban abin al’ajabi. A cikin wata ɗaya, daga Satumba zuwa Oktoba na 2008, dalar Amurka ɗaya ta koma Z$90,000, bayan wata ɗaya, dala ta koma Z$1,200,000, bayan wata guda ya zam sai kana da miliyan sittin (Z$60m) kafin ka sami dala ɗaya tak na Amurka. Kafin Disamba ta ƙare duk a cikin shekarar 2008, dalar Amurka ɗaya ta koma biliyan biyu (Z$2000,000,000).
Ba ka ji komai ba tukunna, abin bai tsaya nan ba, sai da ta kai a farkon watan Janairu na shekarar 2009, ana sayen dalar Amurla ɗaya akan tiriliyan ɗaya na kuɗin Zimbabwe, a watan Fabrairu abin ya wuce hankalin kowa, dala ɗaya ta Amurka ta kai tiriliyan 300. Daga nan Zimbabuwe su ka haƙura da buga kuɗi, su ka ce kowa ya nemi kuɗin ƙasar waje a cigaba da cinikayya da su. Saboda sun buga takarda ɗaya ta Z$100,000, sun buga Z$500,000, sun buga takardar biliyan goma har ma su ka buga takarda ɗaya ta Z$100,000,000,000,000. (Tiriliyan ɗari)
Faɗuwar darajar kuɗin ya jefa ƙasar cikin mawuyacin hali, yadda farashin kaya ya kan ninku cikin abin da bai fi awanni ba. Yanzu za ka sayi abu da safe idan ka koma da yamma sai ka sami kudin ya ninku, zuwa wayewar gari ya ƙara ninkuwa. Kuma duk da ana biyan ma’aikata tiriliyoyin kuɗi amma ba su fi kuɗin sufuri na wuni ɗaya ko biyu ba. Sai ka ga an sayi kofin shayi ɗaya akan tiriliyan ɗari. Da yawan mutane da ƙyar su ke samu su ci sau ɗaya a wuni. Komai ya tsaya cik, ma su saye da sayarwa su ka ruɗe, aka rasa me za a saya ko a sayar, saboda kasuwar ta rikice ta rasa alƙibla. Duk da an sami sauƙin al’amarin daga baya, amma kuma matsalar ta sake dawowa bayan ɓullar cutar Korona.
Irin wannan mummunan tsadar rayuwa da karyewar tattalin arziki ya taɓa manyan ƙasashen duniya kamar su Sin (China) a shekarar 1949, Girka (Greece) a 1944, Jamus (Germany) a 1923, Armeniya a 1993, Hungary a 1946 sai kuma Venezuela ma su arzikin man fetur su ka ɗanɗana irin abin da Zimbabuwe su ka ɗanɗana a baya bayan nan a cikin shekarar 2019.
Na yi wannan rubutun ne saboda a fahimci duk yanayin da mutum ya ke ciki, to wasu sun ɗanɗana fiye da haka, kuma dole Allah Ya jarrabi bayinSa a wasu lokutan, kamar yadda Ya ce: “Lallai ne za mu jarrabe ku da abubuwa na tsoro da yunwa da rashi na dukiya da ƴaƴa da ƴaƴan itatuwa, amma a yi bushara ga ma su haƙuri, waɗanda idan aka jarrabe su da wani bala’i sai su ce. “ان لله وان اليه راجعون” (Quran: 2:155)
Haka kuma, Allah Ya ƙara faɗa mana cewar. “A cikin dukkan tsanani akwai sauƙi” har ma Ya jaddada “Hakika a cikin dukkan tsanani fa akwai wani sauƙi (na tafe)” (Qur’an 94:6-7).
A riƙi addu’a kawai sannan a ƙara godewa Allah.