Farashin siminti ya haura Zuwa Dubu 15,000 A Babban Birnin Tarayya Abuja
Wani bincike da jaridar DAILY POST ta Gudanar A Yau Juma’a a kasuwar Gwarimpa, Area 10, Kubwa, Lugbe da Dawaki, ya nuna cewa buhun simintin Dangote mai nauyin kilogiram 50 ya kai N10,000 sannan simintin BUA ya kai N15,000.
Wani dillali a Gwarimpa, Yinka Adebayo, ya ce farashin simintin Dangote ya kai Naira 10,000 yayin da na BUA ya kai Naira 15,000.
Ya ce ya sayar da buhun siminti kan Naira Dubu 6,000 a watan Janairun 2023 da ya Gabata.
“Muna sayar da simintin Dangote a kan Naira dubu 10,000 kan kowanne buhu, Kuma BUA Muna sai dashi akan Dubu 15,000. Abin takaici, da zai ba ka mamaki cewa na sayar da buhun siminti Guda ɗaya Akan dubu N5,500 Zuwa N6000 a watan da ya Gabata,” inji shi.
Hakazalika, Rukiyat Abdullahi, ‘yar kasuwa a Kubwa, ta ce ana siyar da simintin Dangote kan Naira 10,200 yayin da BUA ke siyar shi kan Naira 16,000.
A Lugbe, dillalan sun tabbatar wa DAILY POST cewa farashin simintin Dangote da BUA sun kai N10,000 da kuma N15,000.
A halin da ake ciki, Ministan Gidaje da Raya Birane, Arc. Musa Dangiwa ya koka kan hauhawar farashin siminti da sauran kayayyakin gini a fadin kasar nan
Ya ce hauhawan farashin abu ne da ba za a amince dashi ba, Don haka ya dage cewa ba za a iya dora laifin kan tashin farashin dala ba.