Labarai

Duk iskanci da lalacewar murja kunya ta tsira saboda masoyiyar Inyass ce – Anisee Futuhi

Advertisment

Wani masoyin Shaik Ibrahim Inyass Alhaji Anisee Futuhu ya bayyana cewa duk kallon ƴar iska da mutane suke yi wa jarumar Tik-Tok murja Ibrahim Kunya shi a wajensa saliha ce kuma yana sonta saboda masoyiyar Inyass ce, “ko da sheɗan ne yake son Inyass ni ma ina son sa balle kuma Murja Kunya”. In ji shi.

Futuhi ya bayyana haka ne ta cikin wani bidiyo wanda Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, inda ya ƙara da cewa “Shehu Ibrahim Inyass ya ce duk wani ɗan iska da mutumin banza ba sa son sa, duk wanda aka ga yana sonsa to mutumin kirki ne. Yadda na tsarkaka haka na tsarkake masoyana gabaɗaya.

Saboda haka, ko da duk Duniya babu wanda ya kai Murja Kunya iskanci ni a wajena mutuniyar kirki ce, malama, kuma sayyada, duk iskancinta ta tsira saboda masoyiyar Shehu Ibrahim Inyass ce”-inji Alhaji Anisee futuhi

Wani labari : Kotu ta tasa ƙeyar Murja kunya zuwa gidan yari

Rundunar Hisbah ta Kano ta ce ta kama ƴar TikTok din nan Murja Kunya tare da saurayinta bisa laifin wallafa wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma waɗanda ba na Musulunci ba a shafin sada zumunta na TikTok.

Makwanni biyu da suka gabata, Hisbah ta ƙaddamar da farautar wasu ƴan Tiktok guda shida waɗanda suka ce suna saɓa wa ka’idojin musulunci a kullum wajen amfani da kafafen sada zumunta.

Kakakin Hisbah Lawal Fagge ya shaida wa BBC HAUSA cewa an kama Murja Kunya da sanyin safiyar Talata, tare da saurayinta.

“Jami’anmu sun kama ta ne a gidanta tare da saurayinta, wanda shi ma yana tare da mu.”

“A baya dai, makwabtanta sun kawo mana korafi game da halinta. A yanzu haka muna kan bincike kafin daukar mataki na gaba,” inji shi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button