Duk da matsin tattalin arziki, IMF ta buƙaci Nijeriya da ta cire tallafin wutar lantarki
Hukumar Bada Lamuni ta Duniya, IMF, ta buƙaci gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da ta cire tallafin wutar lantarki gaba dayan sa.
Wannan kira na zuwa ne bayan da ƙasar ke fuskantar matsanancin matsin tattalin arziki tun bayan da aka cire tallafin man fetur a watan Mayun Bara.
Daily Nigerian hausa na ruwaito a wani rahoto da ta saki na yin duba kan hada-hadar kudade, PFA, IMF ta ce nauyi ya yi wa Nijeriya yawa, inda ta bada shawarar a cire tallafin wutar lantarki gaba dayan sa kamar yadda aka yi wa man fetur.
IMF ta ce wannan shawarar wani mataki ne na farfaɗo da daidaito na tattalin arzikin Nijeriya, bayan da ta koka cewa a bara ta kashe Naira biliyan 375.8 na tallafi bayan da masu shan wutar lantarki su ka iya biyan Naira biliyan 782.6. a lokacin.
Bayan ta yaba wa gwamnatin taraiya bisa kokarin farfaɗo da tattalin arziki da ta ke yi, IMF ta jaddada cewa cire takkafin mai da na wutar lantarki shine mafita.