Duhu a manyan biranen Nijeriya yayin da tashoshin samar da wutar lantarki na samu tangarɗa
Tashoshin samar da wutar lantarkin Najeriya a ranar Lahadi sun sake daina aiki a karo ta biyu cikin wata ɗaya inda ta jefa garuruwa da dama ciki har da Abuja babban birnin kasar cikin duhu.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja (AEDC) ya sanar ranar Lahadi cewa rugujewar ta faru ne da misalin karfe 11 na safe.
“Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Abuja (AEDC) tana son sanar da abokan cinikinta masu daraja cewa matsalar wutar lantarkin da ake fuskanta ya samo asali ne sakamakon rugujewar wutar lantarki na kasa da ya sa ba za a iya samun wuta ba yanzu. Da zarar an samu nasibi za a samar da wutan.
Rugujewar ta baya-bayan nan dai ta faru ne kasa da watanni biyu bayan rugujewar na kasa a watan Disamba da kuma jefa ‘yan Najeriya cikin duhu.
Premium Times hausa na ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne gwamnatin Najeriya ta danganta matsalar rashin wutar lantarki a kasar da karancin iskar gas ga kamfanonin da ke samar da wutar lantarki (GenCos).
Ministan Makamashi Adebayo Adelabu ne ya bayyana haka, cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin sa X, a ranar Juma’a.
“Jiya mun zauna da kamfanonin samar da wuta, wato Gencos, domin lalubo hanyoyin da za mu magance yawan ɗauke wuta a wasu sassan ƙasar nan.
An samu ƙarin wutar lantarki a lokacin Kirsimeti da Sabuwar Shekara, sai dai kuma abin takaici an samu koma-baya a cikin sabuwar shekara.
“Bayan mun gudanar da bincike, sai muka gano cewa rashin samun wutar wadatacciya na da alaƙa da ƙarancin gas ga kamfanonin da ke samar da wutar,” inji ministan.
Yayin da ake fama da matsalar ƙarancin wutar lantarki, har yau masu biyan kuɗin wutar lantarki a Najeriya ba su kai mutum miliyan 12 ba, kamar yadda wani binciken da NBS ya gudanar ya nuna.
Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa, NBS ta bayyana cewa yawan masu biyan kuɗin wutar lantarki ya ƙaru da mutum 240,000 a tsakiyar 2023, inda adadin yawan ya tashi daga miliyan 11.47 zuwa miliyan 11.71.
Wannan ƙididdiga dai ta na nufin har yanzu masu biyan kuɗin wutar lantarki ba su kai mutum miliyan 12 har zuwa ƙarshen 2023 ba.
A ranar Alhamis NBS ta fitar da wannan ƙididdiga a Abuja, mai nuna cewa daga watannin tsakiyar 2023 zuwa watannin kusa da na ƙarshen 2023 an samu ƙarin masu biyan kuɗin wutar lantarki da kaso 2.08 bisa 100.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an yi wannan ƙididdigar bisa ma’aunin yawan bila-bilan biyan kuɗin wutar lantarki, yawan kuɗaɗen shigar da aka samu a watannin da kuma ƙididdigar yawan kwastomomin kamfanonin sayar da wutar lantarki, wato Discos.
Rahoton ya ce an samu ƙarin yawan masu biyan kuɗin wutar lantarki idan aka kwatanta da yawan su a Disamba ɗin 2022, inda a lokacin mutum miliyan 10.94 ne.
Hakan na nuni da cewa an samu ƙarin yawan mutum har kashi 7.09 bisa 100 kenan, daga Disamba 2022 zuwa Disamba 2023.