Labarai

Ba Alkali ne ya bayar da belin Murja Kunya ba – Cewar Kakakin Kotunan Shari’ar Musulunci

Mai magana da yawun kotunan shari’ar musulunci na jihar Kano Muzammil Ado Fagge, ya ce basu da masaniyar fitar da Murja Ibrahim Kunya, daga cikin gidan ajiya da gyaran hali.

Muzammil Ado Fagge ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da menam labarai a yau Lahadi, ya ce a iya sanin su a zaman kotun makon da ya gabata, alkali ya aike da Murja gidan gyaran hali ne har zuwa ranar Talata 20 ga watan da muke ciki domin duba yiyuwar bayar da ita belin ko kuma akasin haka, kamar yadda dalafm na ruwaito.

“Kamar yadda ku ka ji cewar ta fita daga cikin gidan gyaran halin mu ma labarin fitar ta muka ji, amma dai har yanzu alkali bai bada belin ta ba, “in ji Muzammil Fagge”.

Ya kara da cewa a yadda suka sani har kawo yanzu Murja Kunya tana cikin gidan gyaran hali kamar yadda yake a shari’a, amma dai bai yi mamaki ba idan an ce an bayar da ita Beli.

Sa dai a zantawar gidan rediyon Dala FM Kano da mai magana da yawun gidan ajiya da gyaran hali na jihar Kano SC Musbahu Lawan Kofar Nassarawa, a ranar Lahadin nan ya ce, kamar yadda suka samu takardar ajiye Murja, haka suka samu takardar sakin ta hakan ya sa suka sallame ta amma dai ba guduwa ta yi ba.

Al’umma dai na ci gaba da bayyana albarkacin bakin su akan yadda akayi zargin jarumar Tik-Tok din tayi batan dabo daga cikin gidan ajiya da gyaran hali, bayan da babban kotun shari’ar muslunci dake zamanta a Gama ta aike da ita bayan da hukumar Hisbah ta Kano ta gurfanar da ita a gaban ta bisa zarginta da yada badala.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button