Labarai

Kotu ta tasa ƙeyar Murja kunya zuwa gidan yari

Rundunar Hisbah ta Kano ta ce ta kama ƴar TikTok din nan Murja Kunya tare da saurayinta bisa laifin wallafa wasu abubuwan da ba su dace ba da kuma waɗanda ba na Musulunci ba a shafin sada zumunta na TikTok.

Makwanni biyu da suka gabata, Hisbah ta ƙaddamar da farautar wasu ƴan Tiktok guda shida waɗanda suka ce suna saɓa wa ka’idojin musulunci a kullum wajen amfani da kafafen sada zumunta.

Kakakin Hisbah Lawal Fagge ya shaida wa BBC HAUSA cewa an kama Murja Kunya da sanyin safiyar Talata, tare da saurayinta.

“Jami’anmu sun kama ta ne a gidanta tare da saurayinta, wanda shi ma yana tare da mu.”

“A baya dai, makwabtanta sun kawo mana korafi game da halinta. A yanzu haka muna kan bincike kafin daukar mataki na gaba,” inji shi.

Ana zargin Murja da yin amfani da kalaman ɓatanci da rashin kunya a cikin bidiyonta, wanda dubban mutane ke kallo.

Ba ta ce uffan ba kan wannan zargi, amma an gan ta a wani faifan bidiyo da ba a tantance ba yana yawo a shafukan sada zumunta tun bayan kama ta.

A bidiyon, an jiyo ta tana cewa ba ta saci komai ba, kuma ta gode wa Allah a kan hakan.

Kotu ta tura ta gidan gyara hali har zuwa ranar 20 ga Faburairu da za a ci gaba da zaman sauraron shari’ar da ake mata.

Idan ba a manta ba, a watan Nuwamban 2023, hukumar Hisbah ta gayyaci ƴantiktok ɗin da yi musu tayin ɗaura wa dukkan su aure sannan kuma da basu jari don su soma sana’a.

Murja Kunya da wasu abokanta sun halarci wannan taro.

~ Premium Times hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button