Kannywood

An Kama Darakta Sunusi Oscar 442

A safiyar yau ne majiyarmu ta samu wannan labarin daga shafin fitaccen marubucin nan Datti Assalafiy inda ya bayyana faruwar abun kamar yadda ya fada.

Ga abinda yake cewa.

Sunusi Oscar gawurtaccen dan Kwankwasiyya amana ne, a masana’antar Kannywood idan za’a kirga mutum biyar da suka bada gudunmawa wajen kafuwar Gwamnatin Abba to yana cikinsu, kuma yanzu haka yana da mukamin SSA da Gwamnan Kano Abba ya bashi

Sabani ya shiga tsakaninsa da wani SA a cikin Kwankwasiyya, sun dana masa tarko na cin amana sukayi recording muryansa, sukayi kulle-kulle hakan ya jawo aka kamashi ba tare da Gwamna ya sani ba, yanzu haka yana tsare a Abuja kan abinda bai taka kara ya karya ba.

Ni abinda ya ja hankalina shine me yasa har zuwa yanzu Gwamnan Kano Abba ya kasa sasanta hadimansa, har ya bari za’a wulakanta Sunusi Oscar wanda bashi da kamarsa cikin ‘yan Kannywood da suka masa yaki?

Abu daya ne yake burgeni da Sunusi Oscar shine baya raga wa ‘yan Iuwadi da madig0 da suke cikin masana’antar Kannywood, yana yakarsu sosai kuma suma suna yakarsa, shiyasa ma nayi magana, yana daga cikin laifin da yayi kenan wanda yasa ake neman wulakantashi, tabbas ya kamata Gwamnan Kano yayi abinda ya dace

Amma wannan abin kunya ne ga Gwamna ace hadimanka suna rikici kan abinda ba wani abune mai girma ba ya kasa sasantasu har sai an dangana da Abuja, sai dai watakila ko Gwamnan bai sani ba

Allah Ya taimaki abba Gwamna

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button