Labarai

An Gwabza Ƙazamin Faɗa Tsakanin Ɓangarorin Ƴan Bindiga Biyu A JIhar Zamfara

Advertisment

Ƴan Ta’adda Da dama sun mutu a wani kazamar fada Da ya barke tsakaninsu a kauyen Hayin Alhaji da Dajin Munhaye Na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara ta arewacin Najeriya.

Rahotanni sun Bayyana cewa gwabzawar ta faru ne a sakamakon yunkurin da wasu ‘yan bindiga daga jihar Katsina suka yi na yin garkuwa da wasu mazauna kauyukan Zamfara a karshen makon nan.

A Cewar rahotannin bayan da ‘yan bindigar na Katsina suka mamaye kauyukan na Zamfara ne, kasurgumin dan bindigar nan na jihar Ado Alero ya yi Gaggawar kai wa kauyukan dauki don dakile Yunkurinsu na satar jama’a.

An Gwabza Ƙazamin Faɗa Tsakanin Ɓangarorin Ƴan Bindiga Biyu A JIhar Zamfara
Yan bindiga

Shaidun gani da iso sun tabbatarwa manema labarai Cewa a wannan yunkuri an gwabza kazamin fada Tsakanin bangarorin biyu wanda ya kai ga asarar Rayuka, duk da cewa dai bangaren Ado Alero sun Dakile shirin garkuwa da mutanen kauyen.

A halin yanzu, bayanai sun ce mazauna kauyukan da Aka gwabza kazamin fadan sun shirya gudanar da Birne gawarkin ‘yan ta’addan da suka mutun, Wadanda har zuwa yanzu ba a kai ga tantance Adadinsu ba.

Saurari karin bayyani da BBC Hausa na zanta da wasu jami’an tsaro da ke jihar Zamfara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button