Ɓarayin Daji A Birnin Gwari Sun Sha Ruwan Wuta Wotowoto
Boderi da Bodeji Sun Wuce Barzahu Babu Shirin
Wani marubuci a kafar sada zumunta na facebook Muhammad Aminu kabir ya labarto muna labarin yadda rundunar sojojin na nijeriya sun samu gagarumar nasara sosai akan yan ta’addan daji.
Rundunar sojin Najeriya ta 1 division Kaduna tayi nasarar ragargazar ƴan ta’addar daji a ƙananan hukumomin Igabi da Giwa a Birnin Gwari na jihar, sun kuma samu makamai da Alburusai.
Maharan a yankin Maganda-Dausayi – Mugaba sun kai harin ƙwanton bauna ga Jami’an tsaron yayin da suke aikin sintiri, inda suka yi musayar wuta, take Jami’an tsaro suka maida martani.
Faɗan ya ɗauki kimanin awa guda ana fafatawa Inda Jami’an suka kashe ɓarayin guda biyu tare da samun Bindiga 1 ƙirar AK 47 , tare da 1 AK 47 Magazine, 3 rounds of 7.62mm Special, waya 1 ƙirar Techno, Motoci guda 3 ƙirar Hilux da makullan babura, an samu ɗaurin wasu abubuwan da ake zargin marijuana ce ko Wiwi, ƙwayoyin tramadol da kuma tsabar kuɗi Naira 13,200.
Cikin rashin Sa’a ɓarayin sunyi amfani da Shanu domin kai harin Sojojin kuma suka kashe dayawa daga ciki, jamian suna ci gaba da neman ɓarayin da suka gudu.
A wani yunƙurin na Jami’an tsaro wajen kauda ɓata gari, Jami’an na 1 Division a ranar Larabar 22 February 2024, sunyi nasarar farmakar ɓarayin daji a yankin Bada – Riyawa kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, a yayin farmakin Jami’an sunyi nasarar aika ɓarayin guda shidda zuwa barzahu tare da samun Bundigogi 2 ƙirar AK 47 , 5 AK 47 rifle magazines, 300 rounds of 7.62mm Special ammunition da Babura 19.
Wasu bayanan sirri sun nuna cewa ƙasurgumin ɗan ta’addar nan mai suna Boderi wanda ya kitsa satar yara ƴan mata daga Makarantar Yauri, da Kuma jami’ar Greenfield Kaduna da harin ta’addanci da aka kai a Nigerian Defence Academy ya ƙwanta dama, tare da wani babban yaron shi mai suna Bodejo Jami’an na ƙoƙarin tabbas da sahihancin waɗannan maharan da aka kashe.