Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari A Kan Hanyar Batsari Zuwa Jibia A Jihar Katsina

Lamarin tsaro ya zamo babba barazana da tashin hankali a arewacin Nijeriya da rai bai zamo komai ba duba da irin yadda anka maida kashe mutum ba, bakin komai ba , ya Allah mun tuba ka dubemu da rahamarsa wannan wani mummunan labari ne wanda Muhammad aminu kabir da yake kokari wajen tattaro mana bayyanai akan sanin halin da yan uwan mu suke ciki.

Bayanai da muke samu sun bayyana cewa Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai, sun kai mummunan hari a kan hanyar Batsari zuwa Jibia.

A ranar Lahadi 11-02-2024 da misalin 06:00pm na yamma ƴan bindiga suka tare motocin ƴan kasuwa da suka dawo daga kasuwar Jibia akan hanyar su ta zuwa Batsari, inda suka buɗe ma motoci biyu wuta suka kashe mutane Takwas (8) nan take sannan suka ƙone motocin, idan ba’a manta ba ko cikin watan da ya gabata haka Ɓarayin suka tare wata mota ɗauke da kayan Amare suka kashe Direba da yaron shi tare da ƙone motar da kayan dake cikin ta.

Wannan hanya dai bin ta ya zama tashin hankali tamkar ba a cikin Najeriya take ba, akwai buƙatar hukumomi su maida hankali akan wannan hanyar miyasa hakan yake yawan faruwa minene abinda ya Sha Bamban akan wannan hanyar da ƴan ta’addar nan suke ma Al’umma kisan wulakanci.

Wannan hanya dai kusan za’a ce ƙauyukan dake wurin mafi akasarin su manoma ne da suke noma haiƙan miyasa ake yawan kai masu hari.

Ko a lokacin yaƙin neman zaɓe Gwamna Umar Dikko Radda ya yi bugun gaba cewa yabi wannan hanya da ta gagara a bita yana da kyau mai girma Gwamna a maida hankali a wannan hanyar irin yadda akayi yayin da ake yaƙin neman zaɓe.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button