Ƴan bindiga sun kai hari a wurma sun ƙona gidadje, asibiti da ofishin yan sanda da sace mutum 12
A Ranar Litinin din da ta gabata, bayan Sallar Magriba, gungun ‘yan bindiga akan babura suka afka cikin garin Wurma, a Ƙaramar Hukumar Kurfi a jihar Katsina.
Maharan sun banka wa ofishin ‘yan sanda da wani sabon asibitin kula da marasa lafiya wuta.
Haka kuma sun banka wa gidajen mazauna garin wuta da dama. ‘Yan bindigar sun kuma ƙone motoci duk a cikin daren.
Premium Times Hausa ta ruwaito sun ruwaito cewa ,Mazauna garin sun tabbatar wa wakilin mu cewa sun arce da mutum 12.
Wata majiya ta shaida wa wakilin mu cewa maharan sun afka wa garin Wurma da ke yamma da Birchi su na kan babura, ƙoƙarin babura 25, kowane ɗauke da mutum uku da bindigogi. Hakan ya nuna cewa ‘yan bindigar za su kai 75 kenan.
Baya ga gidaje, asibiti, motoci da ofishin ‘yan sanda da aka ƙone ƙurmus, sun kuma banka wa shagunan kayan masarufi wuta a garin.
“Daga garin Birchi da ‘Yarwashe ana hangen wuta na ci a cikin garin Wurma, wajen 8:30 na dare.” Haka wata majiya ta sanar da wakilin mu, wanda ya ce shi ya ma hangi wutar na ci.
Sun shiga garin bayan ƙarfe 7 na dare, suka riƙa harbin kan-mai-uwa-da-wabi.
Hakan ya sa jama’a kowa a fice a guje. Daga nan suka doshi ofishin ‘yan sanda suka banka masa wuta. Sai kuma suka yi wa sabon asibitin duba marasa lafiya a matakin farko, shi ma suka banka masa wuta.
“Yan sandan da ke wurin sun nuna jarunta, amma sai ‘yan ta’addar suka yi masu abin da ake cewa ‘sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi’, saboda maharan sun fi su manyan bindigogi.” Haka wani a cikin manyan garin ya shaida wa wakilin mu.
Ya ce mazauna garin Wurma sun lissafa mutum 12 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da mata da ƙananan yara. Amma dai ba a kashe ko mutum ɗaya ba.
Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Katsina, Abubakar Sadik Aliyu bai amsa kiran da wakilin mu ya yi masa ba.
~Premium Times Hausa