Labarai

ZARGIN ALMUNDAHAH DA KATUTU DA HAKIN AL’UMMA: EFCC ta riƙe fasfunan Betta, Sadiya da na Halima

Advertisment

PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa EFCC ta tsare Sadiya, tsohuwar Ministar Ayyukan Agaji da Jinƙai, bisa zargin gidogar Naira biliyan 37.1.

Hukumar EFCC ta tabbatar da cewa ta tsare tsohuwar Ministar Harkokin Agaji, Jinƙai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq.

An tsare ta ne domin yi mata tambayoyi dangane da zargin salwantar Naira biliyan 37.1 na kuɗaɗen tallafin marasa galihu, a zamanin ta na minista.

Sadiya ta isa hedikwatar EFCC a Abuja, bisa wata gayyatar da aka yi mata dangane da binciken da ake kan yi.

Advertisment

Zuwan Sadiya ke da wuya a ranar Litinin, sai EFCC suka tsare ta bayan yi mata tambayoyi.

Lokacin da isa Hedikwatar EFCC, ta wallafa a shafin ta na Tiwita cewa ta isa ofishin ƙarfe 10.17.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar wa wakilin mu cewa, “Sadiya Umar Farouk ta iso ofishin mu da safiyar yau Litinin.”

Binciken da ake yi mata na da nasaba da wasu maƙudan kuɗaɗe har Naira biliyan 37.1, waɗanda ake zargin an ma’aikatan hukumar ne suka karkatar da kuɗaɗen a zamanin mulkin ta.

Kafin tsare Sadiya, cikin makon jiya EFCC ta sharara wa wata mai suna Halima Shehu tambayoyi bayan an dakatar da ita daga Babbar Kodinetar Raba Tallafin Marasa Galihu ta Ƙasa, wato Shirin NSIPA, wanda ke ƙarƙashin Ma’aikatar Agaji da Jinƙai.

EFCC ta tsare Halima bayan jami’an hukumar sun kai samame ofishin NSIPA a rukunin ofisoshin Gwamnantin Tarayya da ke Abuja, a ranar 2 ga Janairu.

An tsare ta ana yi mata tambayoyi, har sai washegari aka sake ta a bisa sharaɗin beli.

Halima wadda Shugaba Bola Tinubu ya dakatar, ita ce jagorar raba wa marasa galihu kuɗaɗen rage raɗaɗin talauci, waɗanda ake turawa a asusun banki, a ƙarƙashin Shirin CCTP a zamanin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.

A yanzu an maye gurbin ta da wani mai suna Akindele Egbuwalo, a matsayin jagoran shirin na wucin-gadi.

Daga nan ne EFCC ta gayyaci Sadiya, amma ta nemi a sa mata wata ranar.

Lokacin da aka fara fallasa harƙallar da ake zargin an bankaɗo a Ma’aikatar Harkokin Agaji da Jinƙai, sai tsohuwar minista Sadiya ta shiga shafin ta na Tiwita ta nesanta kan ta daga zargin, kuma ta ce wanda ake zargin an danƙara Naira biliyan 37.1 a asusun bankin sa, ba ta ma san shi ba. Shi dai mutumin sunan sa James Okwete. Ta ce kuma ba ta ma taɓa aiki da shi ba.

Ko a cikin 2020 sai da ICPC ta bayyana cewa ta bankaɗo yadda aka karkatar da Naira biliyan 2.67 na kuɗaɗen ciyar da ɗalibai a lokacin kullen korona.

~PREMIUM TIMES

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button