Hukumar Hisba a jihar Katsina ta ja kunnen iyaye akan su kula da yaransu, kuma su ja kunnensu kafin su fara kai samame a gidajen baɗala a jihar.
Kwamandan hukumar Sheikh Aminu Usman Abu-Ammar ne ya faɗi hakan a cikin wani faifan bidiyo yana mai cewa duk mahaifin da ya san ɗansa yana tattara daba a cikin unguwanni, to su kuka da kansu.


Dclhausa na ruwaito cewa Abu-ammar ya ce duk ɗan da ya kuskura ko mahaifin da ya sake ya shigo hannun hukumar zai fuskanci fushin hukuma.
“Zamu shiga lungu da sako domin mu tsawatar, ayi dai-dai”
“Aikin hukumar Hisba ne umarnin da kyakkyawa da kuma hani da mummuna, wannan shi ne jigon aikin hukumar’
Ya kara da cewa “Manufar hukumar shi ne a taimake ka ɗan ka ya zama ingantacce, saboda nauyi ne na hukuma ta yi aikin da za ta inganta al’ummar da take jagoranta.”
Kwamandan ya kara da cewa hukumar za ta yi kokari wajen taƙaita barace-batace a bisa titunan jihar.
Wani labari : Farashin Kayan Abinci A Kasuwar Batsari A Jihar Katsina
A yau ma kamar kullum kasuwar Batsari taci a cikin yardar Allah a inda baki daga ko’ina a kasar nan suka samu halartar kasuwar duba da yadda ake ta kara samun zaman lahiya a yankin har jami’an KCWC Gwaman Katsina Dikko Radda suna ta bada himmarsu wurin ganin komai yana tafiya yadda ya kamata a kasuwar.
To a yauma ga wasu daga cikin farashin kayayyakin masarufi da dai sauran abubuwa kamar yadda aka saba kawowa.
Kayan Abinci;
Buhun Shinkahwar Nigeria 86000
Buhun Masara Fara 50000
Buhun Jar Masara 52000
Buhun Jar Dawa 40000
Buhun Farar Dawa 39000
Buhun Waken Suya 45000 zuwa sama
Buhun Farin Wake Kanana 64000
Buhun Farin Wake Manya har 70000
Kayan Cefane;
Buhun Busasshen Tattasai 65000 zuwa sama
Solon Tattasai Danye 14000
Solon Attaruhu 13000 zuwa sama
Damen Albasa daga 2000 zuwa sama
Kwandon Tumatir daga 2000 zuwa sama
Sauran kayayyakin;
Buhun Rogo kwara-kwara 36000 zuwa sama
Buhun Rogo mai hula 40000 zuwa sama
Buhun Rogo mai hula gari 50000 zuwa sama
Buhun Dankali 11000 zuwa sama
Buhun Auduga duk kilo 450
Buhun Zobo duk kilo 950
Buhun Goruba 4000 zuwa sama
Mai Rubutawa Alhajin Queen
Daukar Nauyi Batsari Peaples Forum (BAPFO).