‘Yan Sanda Sun Cafke Buhunan Tabar Wiwi 45 A Jihar Katsina
Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina karkashin jagorancin CP Aliyu Abubakar Musa, tayi nasarar kama wani matashi da ake zargin sa da sayar da tabar wiwi a karamar hukumar Malumfashi dake a jihar.
Kakakin rundunar ASP Sadiq Abubakar ne ya bayyana hakan a hedkwatar yan sandan ta Katsina.
Yace “A ranar 3/1/2024 da misalin karfe 1 na rana, rundunar ta samu wani rahoton sirri, nan take baturen yan sandan yankin suka kai samame gidan.
“Rundunar tayi nasarar kama Muhammad Isma’il, ɗan shekaru talatin da haihuwa, wanda yake zaune a unguwar BCJA a karamar hukumar Malumfashi.”
“Ana zargin sa da ta’ammali da miyagun kwayoyi, an sami Muhammad Isma’il da Buhunan Tabar Wiwi har guda 45, sai kwalabe guda 500 na sifirit dadi da wasu kwayoyi.”
Kakakin ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin sa, dai-dai ya ambaci wani mutum mai suna Ibrahim Kisko, wanda yanzu haka rundunar na neman sa ruwa a jallo.
Daga karshe rundunar ta hannunta shi da hukumar dake hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta jihar Katsina, domin gudanar da bincike.