Labarai

Yan bindigar da suka sace mutane 31 a ƙauyen Tashar-nagulle, sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 60 a jihar Katsina

Yan bindigar da suka sace mutane 31 a ƙauyen Tashar-nagulle, sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 60 a jihar Katsina

Yan bindigar da suka sace mutane 31 a kauyen Tashar Nagulle cikin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina sun ce ba za su sako wadannan mutanen ba sai an ba su kudin fansa Naira milyan 60 kamar yadda Premiums Times ta ruwaito.Yan bindigar da suka sace mutane 31 a ƙauyen Tashar-nagulle, sun nemi kuɗin fansa Naira miliyan 60 a jihar Katsina

A daren ranar Lahadin da ta gabata ne dai wasu mahara dauke da makamai sun afka kauyen Tashar Nagulle sanye da kayan sojoji, inda suka yaudari al’ummar kauyen cewa su jami’an tsaro ne an turo su ne su kare rayukansu. Sai da mutanen kauyen suka nutsu, sai suka tattara su suka nufi daji su.

‘Yan bindigar dai sun yi amfani da wayar daya daga cikin mutanen da aka sace, suka kira iyalansa, suka nemi da su kai wa Mai Unguwar kauyen don su yi magana da shi.

Wanda suka buƙaci a basu kuɗi Naira miliyan 60 ma damar ana buƙatar su sako mutanen da suka yi garkuwa dasu a daji.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button