Labarai

Yan bindiga sun sace ɗalibai Mata a Jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina

Advertisment

Wasu ƴan bindiga sun sace ɗalibai mata su 2 a jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina kamar yadda Katsina Post ta samu cewa, waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun haɗa da Habiba Ango Shantali, da kuma Maryam Abubakar Musa, waɗanda dukkan su ‘yan asalin jihar Neja ne.

Lamarin ya faru ne yayin da ɗaliban ke kan hanyar su ta dawowa makarantar a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu na shekarar 2024.Yan bindiga sun sace ɗalibai Mata a Jami’ar Al-Qalam dake jihar Katsina

Shugaban Ƙungiyar Ɗaliban Jihar Neja (NANISS) na ƙasa, Kwamared Gambo Idris Shehu, shi ne ya tabbatar da sace ɗaliban a wata sanarwa da Sakatare-janar na ƙungiyar, Kwamared Mohammed Ibrahim ya fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mun samu labarin sace wasu ɗalibanmu biyu na jihar Neja da ke karatu a Jami’ar Al-Qalam a jibar Katsina a kan hanyarsu ta komawa makaranta”.

Advertisment

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button