Labarai

Wata mata ta haifi ƴan-shida bayan shekaru 13 da aure bata haihu ba

Wata ƴar kasuwa mai suna Precious Ifeanyi da ta yi aure shekara 13 da su ka gabata ta haifi ƴaƴa shida rigis a babban asibitin ƙasa da ke Abuja a shekaranjiya Litinin.

Misis Ifeanyi, ƴar asalin jihar Ebonyi da ke karamar hukumar Ohaozara ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa a yau Laraba a Abuja cewa ta haifi jariran, mata hudu da maza biyu, bayan an yi mata aikin dashen ƙwan haihuwa, wato In-Vitro Fertilisation, IVF.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito cewa, a karon farko da mahaifiyar, wacce aka ciro mata santala-santalan jariran nata bayan makonni 30 ta ce a zahiri tana tsammanin za ta haifi ƴan huɗu, amma lokacin haihuwa sai ta ga cewa ashe ƴan-shida ne.

Wata mata ta haifi ƴan-shida bayan shekaru 13 da aure bata haihu ba
Wata mata ta haifi ƴan-shida bayan shekaru 13 da aure bata haihu ba

Da take ba da labarin yadda abin ya faru, ta ce ta yi aure a ranar 3 ga Afrilu, 2010 kamar kowane mutum kuma tana sa ran za ta fara haihuwa nan take.

“Duk da haka, tun lokacin ba a samu sauki ba. Mun yi tsammanin ƴaƴa amma ba su samu ba; mun je wurare da yawa mun kashe kudi maƙudai amma babu sakamako don haka kawai sai mu ka zurawa sarautar Allah ido.

“Sai ga shi yanzu, Allah cikin rahamarSa marar iyaka ya azurta mu, kuma ga mu yau, Allah ya canza lamarin.”

Maijegon, wacce ke cike da farin ciki ta shaida wa NAN cewa a cikin shekaru 13 da ta kwashe tana neman haihuwa, ita da mijinta, wanda Fasto ne a Living Faith Church, Chikara a jihar Kogi, sun kashe makudan kudade amma ba a samu sakamako ba.

Ta bayyana cewa shi ma mijin na ta ya yi matuƙar farin cikin samun haihuwar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button