Wasan kwaikwayo a hukumar hisbah – Maje El-hajeej hotoro
Bayan fitar da sanarwa ana neman wasu shahararren yan tiktok da hukumar hisbah ta kano ta fitar cewa ana neman su bayan cewa wasu daga cikin sun fito suna fadin cewa an san inda suke babu wanda yazo kamunsu ko sammaci ko kiran waya, bayan irin wadannan bidiyo sai gashi kuma mataimakin kwamandan hisbah ya fito da cewa akwai yiyuwar za’a kulle akawun dinsu a tiktok.
Wani marubuci mai suna Maje El-hajeej hotoro yayi wani rubutu wanda yayiwa hukumar hisbah wankin babban bargo inda ya wallafa a shafinsa na facebook yake cewa.
A kwanakin baya muka riƙa rangaɗawa hukumar Hisbah ta jihar Kano guɗa akan yadda suka riƙa samame tare da garƙame mata masu gantali.
Yanzu kuma sai ga shi muna zargin hukumar da nuna wariya ga wasu yan lele da suke da kusanci da gwamnati akan laifin da ya ninka na waɗancan da aka kama aka yaɗa su a duniya kowa ya ga fuskokinsu.-
Wadannan yan lele sun shahara wajen yaɗa batsa da ayyukan fasadi ƙarara ba tare da shakka ko kunya ba.. Amma tunda gwamna ya hau munbarin siyasa ya shafe mintuna yana yabon jagorar yaɗa ɓarnar mutane suka yanke ƙauna da ɗaukar matakan ladabtarwa akan ta.
Wani babban wasan kwaikwayo da ya bayyana kwanan nan shine yadda aka yaɗa labarai cewa Hisbah na neman waɗannan tatattun marasa kunya.
Amma sai ga shi cike da ƙwarin gwiwa tana cika bakin ƙaryata wannan maganar tana ma nuna ba a isa a kama ta ba. Shima sai ga ɗayan yana fadin kullum sai ya je Hisbah ya ci wainar fulawa su aminan juna ne.
Daga ɓangaren Hisbah kuma sai ga bidiyo suma fadin wai babban daraktan Hukumar ya yi magana da mai kamfanin Tiktok wai za a rufe musu account idan ba su daina ba.
Ku da kuke tare da su ba ku iya daukar mataki akansu ba sai kun je wajen shugaban kamfanin Tiktok? Yan a daidaita sahu da kuke kamawa kuna yi musu aski su ba ya’ya ba ne?
Ko su matan da kuka kama da sunan gantali ba haifar su aka yi ba? Da wanda ya je yawo aka kama shi da wanda ya ke yaɗa ɓarna a duniya wa ya fi muni?
A baya an yi ta sukar gwamnatin baya da sanya siyasa a sha’anin shugabancin hukumar Hisbah don haka ya dace a rika adalci wajen hukunta kowa ba tare da an kalli alaƙarsa da gwamnati ba.