Labarai

Wani Matashi ya kirkiri injin ban ruwa noma rani da baya bukatar hasken rana ko man fetur

Advertisment

Matashin mai suna Malik Muhammad Kumo, ɗan asalin jihar Gombe ya zabi samar da injin bayin ne domin hucewa al’ummar yankunan karkara takaicin tsadar man fetur da kuma tsadar inji mai amfani da hasken rana.

Wani Matashi ya kirkiri injin ban ruwa noma rana da baya bukatar hasken rana ko man fetur
Wannan shine injin da Engr. Malik ya hada

Malik Muhammad dai ya hada irin wannan inji da ke samar da ruwa ta hanyar amfani da batirin mota da wasu injuna da koyel, inji yana tashi da key kamar yadda ake tada mota, yana diri yana chajin batir har lokacin da ka gaji ka kashe shi, yana awa saba’in da biyu ba tare da an kashe shi ba, a jikin sa harda wajen saka chaji na waya.

Wani Matashi ya kirkiri injin ban ruwa noma rana da baya bukatar hasken rana ko man fetur
Injin na ban ruwan noman rani da engr.malik ya kirkira

Wannan mataki nasa ya sa mutane da dama a yankunan karkara sha’awar noman rani, wanda ya zama sana’a a wajen mutane.

A cewar Malik Muhammad Kumo, abun alfahari ne a gare shi, wanda hakan wata babbar nasara ce da yake alfahari da ita ta sanadin mahaifinsa.

Sai dai duk da cewa wannan matashin ya ce ya samu nasarori masu yawa a baya a irin wannan fannin kirkire-kirkire, sai dai kuma akwai tarin kalubale da yake fuskanta musamman rashin kuɗi, wanda yasa ya share tsawon wata uku yana fama wajen ganin ya haɗa wannan injin a cewar sa.

Daga karshe dai yayi kira ga matasa da su yi amfani da basirar da suke da ita wajen dogoro da kansu ba tare da sai gomnati ta basu aiki ba.

Matashin yayiwa Allah godiya bisa nasarar da ya samu na samar da wannan injin inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta facebook Malik Muhammad Kumo

Allahamdulillah
Allahamdulillah

Wannan yana daya daga cikin Construction da Allah yabamu ikon gama hadashi a yau wato engine noman rani wato (DC water pump)

Wannan Engine baya bukatan petur, gas KO hasken rana.

Wannan engine shiyake mawa kansa chaji batare da hasken rana ko wutar lantarki ba.

Wannan engine yana iya 72hrs batareda an kashe ba.

Wannan engine yana bada ruwa liter 3600 per minute

Wannan engine mun masa gun yin chajin waya ajikinsa.

Sauran bayanai zasuzo nan gaba akan wannan engine.

I’m ENG. ABDULMALIK KUMO
Malik Muhammad Kumo”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button