Labarai

Wani matashi ya bada labarin yadda mahaifinsa yayi abota da musulmi har ya karbi Musulunci

Advertisment

Wani matashi mai suna Aliyu Bashir ya bada labarin yadda mahaifinsa yayi abota da wani abokinsa fiye da shekaru hamsin suna abokan juna, har ya karbi kalma shadda Allahu Akbar.

idan kana tare da wanda ba musulmi ba, ka kyautata mu’amala da shi, ba ka san menene gobe zai haifar ba

Fiye da shekaru hamsin da suka wuce, akwai wasu abokan juna guda biyu, suna aiki tare. Ɗayan musulmi ne, shine mai ƙarancin shekaru a tsakaninsu. Ɗaya Kirista ne mai suna Daniel.

Daniel ya koyi addinin kiristanci daga turawan mulkin mallaka, kuma ya haddace wassu ɓangarori na sabon alƙawali sosai. Ya san addininsa da kyau.

Kasancewarsa tare da musulmai a aikin hannu da suke yi ya sa ya ƙara fahimtar musulunci. Ya kula cewa abokin aikinsa yana da mutunci da amana, ga kulawa da addini. A ɗaya bangaren ya kula cewa abinda ya karanta a littafinsa na Bible daban, abinda ake yi da sunan addini daban. Hakan ya sa masa shakka akan gaskiyar addini da yake a kai.Wani matashi ya bada labarin yadda mahaifinsa yayi abota da  musulmi  har ya karbi Musulunci

Watarana yace ma abokinsa: “Hamman, ina so in musulunta.”
Abokinsa Hamman ya ji daɗi sosai, ya ba shi kalmar shahada, shi da matansa da ‘ya’yansa. Daga nan sunansa ya canza daga Daniel zuwa Muhammad Bashir.

Wannan taƙaitaccen tarihin yanda mahaifina Muhammad Bashir ya shiga addinin Musulunci kenan. Ya tasirantu da kyakkyawar mu’amala da ya gani a wajen musulmai da yake kewaye da su, kafin ya tasirantu da aƙidarsu.

Yau shekaru biyu kenan da rasuwarsa, bayan shafe kimanin shekaru 107, fiye da rabin shekarun yayi su a addinin musulunci.

Allah ya kai haske makwancinsa, Amin.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button