Tabarikkah: Dan Napep da ya tsinci wayar iPhone 13 Pro max ya mayar ya samu gagarumar karamawa da kyauta


Wani matashi da munka kawo muku labarinsa da ya tsinci wayar salula iPhone 13 pro max wadda kuɗin ta sunka wuce Naira miliyan daya ta wata yarinya da ya tsinta ya mayar mata abu ta.
Shine wani bayan Allah ya sanya a cigita masa wannan matashin irin kokarin da yayi ya kamata a yaba masa kuɗi ayi masa goma ta arziki.
Shine shafin wake-up katsina youth sunka samu zantawa da matashin akan irin yadda wani bayan Allah ya sanya a nemo mishi wannan yaro, kuma alhamdullahi an samu ga yadda tattaunawar ta kasance kamar yadda shafin ya wallafa.
“A madadin Engr. Tukur Tingilin muna godiya ga daukacin mutanen da suka taya mu samun yin magana da wannan saurayi.
Sanin kowa ne cewa Engr. mutum ne da ya yarda da koyawa matasa kamun kifi, ba wai ba su kifi ba. A haka ne ya yi alkawarin daukar nauyin karatun wannan yaro na duk makarantar da ya ke so ta gaba da sakandare, sannan kuma ya ba shi kyautar kudi a matsayin yabawa.
Mahafin wannan matashi, da mahaifiyarsa, da limamin garinsu, da kuma wasu daga cikin makusantansa, sun kira ni kuma sun nuna jin dadinsu da kuma yi wa MD addu’a.”