Labarai

Rigima ta sanya yayi Ajalin Abokin aikinsa a kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai suna Isma’il James, dan shekara 32, bisa zarginsa da kashe abokin aikinsa a cikin kamfanin sarrafa Buhuna Fas Agro, dake rukunin masana’antu a unguwar Sharada dake jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan SP Abdullahi Kiyawa ne ya sanar da hakan ga gidan rediyon Dala FM kano, da yammacin Lahadin nan, ya ce matashin James ana zarginsa ne da kashe abokin aikin nasa mazaunin unguwar Ja’en Dango dake karamar hukumar Gwale, mai suna Tukur Adamu dan shekara 32, bayan da suka samu rikici a kamfanin.

“Bayan faruwar lamarin ne wasu fusatattun matasa suka yi yunkurin kona kamfanin inda kwamishinan ‘yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel ya baiwa baturen ‘yan sandan Sharada SP Abdulrahim Adamu umarnin kai agajin gaggawa aka kama mutane 13, “in ji SP Kiyawa”.

Ya kuma ce bayan da jami’an mu suka halarci unguwar ne suka dauki matashin inda suka kai shi Asibitin kwararru na Murtala Muhammed dake Kano, daga bisani ne likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Rigima ta sanya yayi Ajalin Abokin aikinsa a kano
Wannan shine Abokin Ismail James Tukur kenan

Yanzu haka dai kwamishinan ‘yan sandan Kano ya bayar da umarnin mayar da matashin babban sashin binciken mayan laifuka na kisan Kai, domin gudanar da bincike tare da daukar mataki na gaba, “A cewar Kiyawa”.

Da yake karin bayani kan kashe Tukur din, matashi James ya ce, rikicin ya samo asali ne biyo bayan yadda suke samun matsala da shi a wajen aiki, amma dai yayi nadamar kashe Tukur din, inda ya ce inda ya san zai yi sanadiyyar mutuwar wani da bai zo Kano ba.

Rahotanni dai sun bayyana cewa bayan zargin kashe Tukur Adamu, mai mata daya da ya’ya biyu ne wasu fusatattun matasa a garin na Ja’en suka je wajejen kamfanin suna ikirarin ayi musu adalci na kashe musu dan uwa da akayi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button