Kannywood

Rahama Sadau ta kafa tarihin da kaf yan kannywood babu,a duniyar fim

Shaharariyar jaruma nan rahama sadau da ke fina finai a hausa fim kannywood da fina finai kudu nollywood, har da ma fina finan indiya Bollywood kenan a can ma tana haskakawa.

Wannan shi kadai tarihi ne wanda ta doke duk wani dan kannywood maza da mata domin itace kawai anka haskakawa a cikin jerin wannan fina finai kannywood, nollywood da Bollywood.Rahama Sadau ta kafa tarihin da kaf yan kannywood babu,a duniyar fim

To ba shine babban tarihin da ta kafa ba, tarihin da ta kafa shine itace ta farko da tayi kokari wajen ganin sai fim dinta mai suna “Mati a Zazzau” ya shiga manhajar ‘Netflix’ wanda shine manhajar da ake sanya fina finai da sunka shahara a duniya .

A shekarar da ta gabata 30th ga watan disamba 2023 ne fim din Mati a Zazzau ya shiga manhajar ‘Netflix’ ta duniya.Rahama Sadau ta kafa tarihin da kaf yan kannywood babu,a duniyar fim

Abu na biyu kuma shine tana daya daga cikin fim din kudancin nijeriya nollywood kenan mai suna “wrath and revenge” wanda shima yana a manhajar ‘Netflix’ wanda anka fara haskaka a 28 ga watan disamba shekarar da ta shude 2023.

Tabbas Rahama sadau ta yi kokari sosai wajen budewa abokan sana’ar ta na Kannywood domin suma suyi fafutuka wajen ganin fim nasu na shiga manhajar ‘Netflix’.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button