Labarai

Miji da mata da ƴaƴansu 5 sun rasu sanadiyar Gobara a jihar kano

Wani magidanci mai suna Shuaibu Iliyasu da matarsa Binta da kuma ƴaƴansu biyar sun rasu a wata gobara da ta tashi tsakar dare a unguwar Tudun Wada a ƙaramar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Mazauna unguwar sun tabbatarwa Daily Nigerian Hausa cewa wutar ta tashi ne bayan ƙarfe 12 na dare a yayin da matan ke tsaka da barci.

A cewar wani mazaunin unguwar, Malam Idi Maikatako, wutar ta tashi ne tun misalin bayan ƙarfe 12 na dare, inda ya yi tsammanin cewa kawo wutar lantarki ne ya haifar da tararratsin wuta da ya kai ga tashin gobarar.

Daily Nigerian hausa na ruwaito cewa ,ya kara da cewa da jin afkuwar lamarin, tuni makota su ka shiga gidan domin kawo ɗauki, inda kafin ayi aune, 7 daga mutanen da ke barci a dakin sun rasu, sai yau ya ɗaya da ta rage, wacce aka garzaya da ita asibiti.

 Miji da mata da ƴaƴansu 5 sun rasu sanadiyar Gobara a jihar kano
Miji da mata da ƴaƴansu 5 sun rasu sanadiyar Gobara a jihar kano Hoto : Daily Nigerian hausa

Jami’an hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta Kano, PFS Saminu Yusif ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya tabbatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon hayakin da ya cika dakin da su ke.

Ya ce sun karbi kiran gaggawa daga wani mazaunin unguwar, Ibrahim Sani da misalin karfe 12:25 na dare cewa wasu ƴan daki daya su bakwai sun rasu sakamakon gobara.

Ya ce da jami’an su na unguwar Dakata su ka isa gidan, sai suka tarar tuni an kashe wutar kuma an fito da mamatan sannan an garzaya da ƴar daya till da ta rage zuwa asibiti.

Ya yi kira ga al’ummar jihar da su rika kashe duk wani soket na wuta idan za a kwanta domin kare faruwar haɗarin wuta.

~Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button