Mayar da wasu ɓangarori na CBN zuwa Legas yana da illa a kan tattalin arzikin Nijeriya – Ahmad Ganga
Wani matashi fitaccen marubuci kuma dan jam’iyar APC Ahmad Ganga yayi wannan sharhi akan wannan babba illar da tattalin arziki Nijeriya zai fara akan kwashe wannan sashen wasu babban bankin Najeriya zuwa Legas.
Mayar da wasu ɓangarori na CBN zuwa Lagos yana da illa a kan economy ɗin Nigeria, amma mafi illa a ciki shi ne ɗauke “Banking Supervision Department” kacokam zuwa Lagos.
Me hakan ke nufi?
Mayar da department na Banking supervision zuwa Lagos na nufin gwama kan bankuna (wanda mafi yawa na yarbawa ne) da masu sanya idanu a kan su (regulators). Hakan zai zamanto tamkar tuwona maina. Kuma Department ɗin ya kasance shi ne jigon aikin CBN. Yayin da duk ka ɗauke shi zuwa Lagos, babu shakka ka ɗauke CBN ne zuwa Lagos.
Kuma a halin yanzu da ake wannan batun, Banking Supervision Department yana da office a Lagos ƙunshe da ma’aikata 94, waƴanda suke gudanar da aikin su on-site. Ma’ana a Bankunan da suke lura da su. Dama kuma saboda Bankunan aka samar da su a Lagos ɗin.
Shi kuma Department ɗin na Abuja yana gudanar da aikin sa ne off-site, ba lallai sai yana kusa da Bankunan ba. Hasali ma ba a tsara aikin off-site kusa da Bankunan ba saboda tabbatuwar ingancin kula da su da ake yi.
Department ɗin na Abuja na ƙunshe da ma’aikata 154 har da Director. Yanzu kuma an ce duk su koma Lagos. Kenan ana nema a rushe aikin off-site, wanda hakan ke nufin babu checks and balances.
Ku san kaso 100 na ma’aikatan Department ɗin dake Lagos Yarbawa ne da sauran ƙabilun mutanen kudancin Ƙasar nan. Yayin da ma’aikatan Abuja suka kasance kaso kusan 65 mutanen Arewa ne. Kun ga kenan a zahiri ma sun fi mutanen mu yawa. Kuma su ke da dukkannin Deputy Directors na Department ɗin, sai Mace ɗaya da ta zamanto ita kaɗai ce daga yankin Arewa, Jahar Nassarawa. An kuma bar ta a nan Abuja ba tare da an bari ta tafi Lagos ba. Wannan ke nuna cewa shugabancin Department ɗin kacokam zai kasance babu ɗan Arewa ko ɗaya, sai Yarbawa da Inyamurai.
Fiye da shekaru 50 da kafuwar CBN, sau 3 aka taɓa samun Ƴan Arewa da suka riƙe Director a Banking Supervision Department. Na yanzu da yake kai acting ne. Kafin ya zama acting ɗin kuma sai da suka ɗauke Ƴan Arewa biyu da suka girmeshi a aiki domin su bashi wajen. Shin me kuke tsammanin zai faru idan Department ɗin kacokam ya koma Lagos?
Wannan matashiya ce kafin mu shiga gundarin da illar ɗauke department ɗin zai janyowa al’ummar Arewa.