Labarina ya Kafa tarihi samun “1million views” cikin awa 24 da ake haskawa a YouTube
Labarina ya kafa tarihin da kam duniyar fim din hausa bai samu na inds da samu sama da miliyan daya a da sunka kalle shi a cikin awa 24.
Labarina shiri ne mai dogon zango wanda anka fara da jarumai kamar haka, mahmud, sumayya, presido,lukman da kuma raba gardama, wanda tun daga zango na farko fim din ya samu karbuwa har yanzu da ake zango na takwasa duba da zango na takwas lissafi ya canza.
An samu wasu sababbin Fuskoki gaba daya daga cikin na zango na farko zuwa na bakwai, to shi wannan wani labari ne da ya samu jarumai kamar haka, Al-amin, faruk, lawan , jamila da maryam wanda anka shiga chakwakiyya sosai.
Labarina zango na takwas zango na shidda ya kafa tarihin da kaf masana’atar shirya fina finai ta kannywood bata samu ba, inda Kashi na shidda kacal ya samu sama da miliyan daya da sunka kalle shi, a manhajar YouTube da ke tashar saira movies
Yan kallo sun jinjinawa malam aminu Saira mai bada umurni wannan shiri tare da haziƙin marubucin shirin labarina Yakubu M. Kumbo tare da masu shiryawa Malam Aminu saira, Nazifi Asnanic da sarkin waka nazir m Ahmad.
Tabbas wannan kashi na shidda “episode 6” zai ya samun makala fiye da yadda muke tunani kafin wani mako mai zuwa da za’a cigaba da fafatawa wanda ita Maryam tace sam bata yarda da Alh. Al-amin mai nasara a matsayin mijin da ta aura ba.