Kannywood

Labarin kyautar motar Maryam Labarina ƙalubali ga ƴan mata masu sha’awar shiga harka fim

Advertisment

Labarin kyautar motar fatima hussaini wadda anka fi sani da maryam labarina da ya kara de shafukan sada zumunta irin duk yaushe ne tauraruwar wannan jaruma, shine wani dan jarida da ake aiki gidan rediya Salisu Baffayo yayi wani sharhi tare da jan hankali ita yarinyar da ta samu wnanan kyautar da sauran yan mata masu sha’awar shiga wannan haka.

Yayi wannan tsokaci ne a shafinsa na facebook inda ya wallafa kamar haka.

Labarin kyautar motar da wani bawan Allah Ya baiwa Fatima Hussaini (Maryam Labarina) na fahimci ƙari ne kan ƙalubalen da ƴan mata ke fuskanta na kwaɗayin shiga harka Fim don neman suna ko samun abin duniya. Matsala ce da ka iya kai wa ga wasu cikin matan aure (masu kwaɗayi) su kashe aurensu domin su gwada ta su sa’ar.

Kai hatta abokan sana’a a Fim ɗin ƙalubale ne garesu domin ko da a ce ta jima a Indostirin to tauraruwarta bata fara haskawa ba sai a shirin Fim ɗin Labarina da ta fara fitowa a ƙasa da watanni biyu. Wanda anan ta tarar da tarin matasa, dattawan mata da maza waɗanda a wasu lokutan sai sun yi da gaske wajen jure wulaƙanci da ƙasƙanci kafin a saka su a Fim ɗin da za a sallame su da kuɗin da ba su wuce Naira dubu 5 zuwa 10 ba.

Advertisment
Labarin kyautar motar Maryam Labarina ƙalubali ga ƴan mata masu sha'awar shiga harka fim
Wannan ita ce motar da anka baiwa Fatima Hussaini wanda ake kira ‘Maryam Labarina’

A gefe guda ga tarin waɗanda lalurar rashin lafiya ta kwantar, suna fama da neman na magani, babu cin yau ballantana na gobe. Waɗanda a ganina su ya kamata a ce ana taimakawa duba da gudanarwar da suka jima suna bayarwa.

Idan kuma kana magana ta burgewa ko tausayawa ga role ɗin da Tauraro ya hau a Fim ne to ina ka bar irin su Malam Kamaye na shirin ‘Daɗin Kowa?’ wanda kamata ya yi a ce yanzu ya rasa idan zai saka kyauta daga masu kallo.

Kai a ma jingine taurari a gefe, ina ka bar Marubuta, Furodusas da Daraktoci?
Shin ba su ne ababan burgewa a matakin farko ba?

Ita ma Maryam ɗin da kamata ya yi a ce ta boye labarin kyautar motar da aka yi mata ko don gudun baki da abin da ka je ya zo.

Allah Ya sa mu dace, Ameen Ya Hayyu Ya Ƙayyum.

Hausaloaded ta tattaro kadan daga cikin martanin mutane.

 

@Nura Yusuf Tsaure cewa yake yi:

Wallahi Salisu nayi mamaki,to idan mutum yayi magana ba kowa zai fahimceshi.
Na farko dai shi Mai kyautar badon Allah yayi ba.Idan don Allah ne akwai marasa lafiya masu zuwa gidajen yada labari kullum da lalurar rashin lafiya da baifi 10,15 ko 20k ba.
Akwai wadanda mabasa iya fitowa su fada ba,ko a makobtansavwlh sai an samu masu buqata kala-kala amma bai kallesu ba.
Kuma lallai masu qaramar fahimta zasu ga wani abin kirki tayi har suyi shaawar kwaikwaya alhali ba gaskiyar halinta bane(wasa ne)
Ita dai duniya gidan rudu ce
Lallai dazai taimaki al’umma a yanayin da ake ciki na matsi a sirrance da Allah ya dubi lamuransa.
Ko ya tafi Islamiyyu ya dinga kyau ta best students da kyautata rayuwar malaman Gina bandakuna da sauransu da ya taimaki kansa.

@Hassan Auwalu Muhammad cewa yake yi :

Salisu Baffayo nida da nine ita da bazan bayyana ba. Ni bana kallon fim din, ban santa bq, amman yadda nake ganin hotunanta a facebook, nan na gane itace ake magana a shirin na labarina, but yadda nake ganin wasu kananun bidiyonta na yawo, na gane tana da rawar kai, kuma yarinya ce karama. Yanzu abun yake mata sugar.

@Nasiru salisu zango cewa yake :

Ku dai Kun Faye magana shi Kamaye wa zai bashi mota bayan bashi da Arzikin man fetur. Ai komai da muhallin sa “An daurawa kuturu ankwa ta sabule “

@Samira Usman Adam cewa take :

Yayana a nemo min form kawai, wannan sabga ai nima na iya.

@Fatima hassan cewa take :

Shima Wanda yabata motar watakila a unguwarsa a layin gidansa amakwaftansa akwai Mai buqatar temako fiyeda tunani,Kuma baza’arasa Mai gudun duniyarba akusa da mahallinsa azahirance kenan ba’a tatsuniyanceba,Amma kawai datayi shiru wllh zaifi bayyana wannan shiriritar datayi domin ni aganina tamakar saurayine yayiwa budurwarsa kyauta meye abin yabawa aci da Kai?

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button