kwankwaso ka iya maye gurbin wike a matsayin ministan abuja
Bayanai Dake fitowa daga fadar shugaban kasar Nigeria, na Nuni da cewa shugaban Kasa Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai yi tankade da rairaya a Gwamnatin sa, musamman ga masu mukaman da basu tabuka abin kirki ba a tsawon lokacin da suka yi akan kujerunsu.


Hausa Reporters ta rawaito cewa, hakan ya biyo bayan wani rahoton sirri da Shugaban kasar ya samu daga masu bibiya da binciken kwakwaf. Inda bayanan nasu ke Nuni da cewa tuni Shugaban kasa ya Shirya tsaf domin yin garambawul, Inda ake zargin ministan Abuja Wike ka Iya komawa Kujerar Jakadan Nigeria a USA, Yayin da Kwankwaso Kuma ka Iya zama sabon Ministan Abuja.
Rahoton ya Kara da cewa Wasu ministocin ka Iya rasa kujerun su baki Daya Yayin da Kuma Wasu ka Iya Samun Sauyin kujera ko Kuma gurin Aiki….
Wani Lanari :Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya raba kwamfutoti da Naira dubu 100,000 ga daliban da suke karantu fannin shari’ah.
Mai girma Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar A. Namadi FCA, ya raba kwamfutocin hannu (laptops) da naira dubu 100,000 ga kowanne daga cikin Dalibai 31 Dake karatu a Makarantar horas da daliban Dake nazari a fannin Shari’ah (Law Schools), baya ga biya musu kudaden makaranta.
.