Kwaɗayi ko Ƙaddara: An tsinci gawar wata mata babu kai a otel
Wani mutum, Auwal Garba ya shaidawa rundunar ‘yan sandan Adamawa cewa shi ne mijin wata mata da aka tsinci gawarta an yanke mata kai ranar Alhamis a wani otel da ke Yola babban birnin jihar,
Mutumin ya ce Shekararsu Shida da aure, sunan ta Bilkisu Alhaji Idi amma auren nasu ya mutu a watan jiya.
Mahanga ta ruwaito a ranar Alhamis ne wani da ake zargin mai yankan kai ne ya kai margayiyar zuwa wani Otel mai suna Happy Day Guest Inn, ya yi mata yan dabaru ya fille kanta ya saka a jaka sannan ya fice daga otal din,
Tun a lokacin ba a iya gano ko wacece matar ba saboda babu kai sai da yammacin ranar Juma’a bayan da labarin ya bazu,
Sai dai tsohon mijin marigayiyar, Auwal Garba, ya tabbatarwa da ‘yan sanda da yammacin jiya cewa marigayiyar wanda ya bayyana sunanta da Bilkisu Alhaji Idi, matarsa amma ya sake ta a watan jiya kuma suna da yaro tsakaninsu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin
Ya ce Garba ya kara da shaida masu cewa “Ko a ranar da zata rasu ma sai da ta kira shi a waya tana son ta yi magana da yaron nata, amma basu samu magana ba kasancewar yaron baya nan sun fita unguwa da kakarsa.”