Labarai

Ina taya Abba Kabir murna kan nasarar da ya samu – Atiku Abubakar

Advertisment

Jagoran adawa a Najeriya, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya taya gwamnonin jihohin da suka samu nasara a kotun ƙolin ƙasar.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, Atiku Abubakar ya ce hukuncin kotun ƙolin ya tabbatar da nasarar al’ummar jihohin Bauchi da Filato da Akwa Ibom da Zamfara, tare da ɗaga martabar dimokraɗiyya a ƙasar.

BBC Hausa na ruwaito Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma miƙa sakon taya murna ga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP kan nasarar da ya samu a kotun ƙolin.

”Wannan hukunci ya ba ni damar tabbatar da ƙudurina na cewa haɗin kan jam’iyyun adawa zai taimaka wajen ƙarfafa dimokraɗiyyar Najeriya”, in ji Atiku.

”Don haka a shirye nake na jagoranci wannan ɓangare, ta hanyar yin aiki tare da shugabanni da gwamnoni don tabbatar da ci gaban ƙasarmu”.

Jagoran adawar ya ci gaba da cewa hukuncin kotun ƙolin ya tabbatar da ƙarfin da jam’iyyarsa ta PDP ke da shi a jihohin da take mulki.

”Ina kira da gwamna Bala Muhammadu na Bauchi da Dauda Lawal na Zamfara da Barista Caleb Muftwang na Filato da Fasto Umo Eno na Akwa Ibom da su ɗauki nasarar da suka samu a kotun ƙolin a matsayin wata dama da za su sake inganta jagorancin da suka riga suka fara kafawa a jihohinsu”, in tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

Ya kuma ce ”ina da yaƙinin cewa jam’iyyarmu ta PDP za ta ci gaba da kasancewa babbar jam’iyyar adawa a ƙasar, da taimakon gwamnoni da kuma ni kaina, a yayin da za mu tunkari kakar zaɓe mai zuwa”.

~Bbchausa

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button