Labarai

In za’ayi gini sau dubu a masallacin Idi ko makaranta sai mun ruguje shi -Kwankwaso

Advertisment

Jagoron darikar kwankwasiyya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi wani takaitaccen bayyani akan rushe rushe da sunkayi a cikin jihar kano wanda abun ya ɗaga hankalin mutane irin ganin yadda ankayi asarar dukiya mai yawa.

A cikin wani faifan bidiyo da gidan rediyo premier Radio 10.27 sunka wallafa a shafinsu jagoran yayi tsokaci inda yake cewa.

Mu abinda munka dauka dai-dai da yawan mutane basu dauke shi dai-dai ba, kuma abinda munka dauka ba dai-dai ba dai-dai da yawan mutane sunka dauka dai-dai, kuma abinda zaka fahimta a nan shine a siyasa abubuwan da ake yi shine dai-dai da kawo cigaba, idan ba dai-dai kake yi ba, ai zaka ga babba matsala ai yanzu da suke ta jawo Abuja suje gari kaza an rushe kaza an waye masallaci.

Wasu ma basa cewa masallaci gine ginen su harda da yan kwankwasiyya a ciki , duk dan kwankwasiyya ko yau ko gobe ko wata rana duk wanda zai saye filin idi ko masallacin juma’a ko masallacin hamsa salawatu to wannan a gurin mu ba dan kwankwasiyya bane.

Kuma in dan kwankwasiyya ne bai ma gane miye kwankwasiyyar ba, wanda idan anzo abu dai-dai yace eh dai-dai ne, idan kuma ba dai-dai bane yace ba dai-dai bane kuma haka muke tafiya.

Kuma shiyasa duk wani mai hankali yake goyon bayan mu.

In za’ayi gini sau dubu a masallacin Idi ko makaranta ko irin wannan wurin aiki hajjin nan kam na addini , duk wani dan kwankwasiyya ganin mu dai-dai a gyara-inji kwankwaso

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button