Farashin shinkafa a Nijeriya ya karu da kashi 81
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta ce an samu ƙari a farashin shinkafa a ƙasar a shekarar 2023.
NBS ta ce farashin kilogiram ɗaya na shinkafa ‘yar gida ya ƙaru da naira 411.76 idan aka kwatanta da 506 da aka sayar da ita a watan Disamban 2022.
Cikin rahoton farashin wasu kayyaki a watan Disamban 2023, da hukumar ta fitar ranar Laraba ya nuna cewwa matsakaicin farashin kilo guda na shinkafar gida a watan Disamban 2023 shi ne naira 917.93.
“Hakan na nufin an samu tashin farashin da kashi 81.35 cikin 100 cikin shekara guda, wato daga naira 506.17 a watan Disamban 2022 zuwa naira 867.18 a watan Nuwamban 2023”, in ji rahoton.
Sai dai manoman shinkafan sun ce ba su mamakin tashin farashin ba, idan aka yi la’akari da tsadar taki da sauran kayayyakin noma da suka fuskanta.
Shugaban ƙungiyar Manoman shinkafa na jihar Jigawa, Alhaji Adamu Maigoro Haruna ya shaida wa BBC cewa a daminar da ta gabatan an samu ƙarancin zubar ruwan sama, haka kuma masu bayi ta hanyar amfani da ruwan koguna, to kogunan ba su da ruwa, suma masu amfani da inji sun fuskancin tsadar man fetur da za su yi amfani da shi wajen tayar da injunan bayi.
”Hakan ya sa aka samu ƙarancin shinkafar a daminar da ta gabata, domin wanda ke tsammanin zai samu buhu 100 dakyar ya samu 20 ko 30”, in ji shi.
Rahoton NBS din ya kuma nuna cewa matsakacin farashin kilo ɗaya na tumaturi ya ƙaru da kashi 77.60 cikin shekara guda, sannan farashin wake ya karu da kashi 48.54, sai farashin jan nama da ya ƙaru da kashi 32.38.