EFCC ta sake bankado da tuhumar badakalar kudi da ake yiwa tsofaffin gwamnoni 13
Hukumar Yaƙi da cin hanci da Rashawa EFCC Ta Sake Dawo da Binciken badakalar Tsofaffin Gwamnoni 13 da Wasu Tsofaffin Ministoci, inda kuɗaɗen suka kai sama da N Biliyan 853, dan jarida Ahmed Tijjani Ramalan ya wallafa a shafinsa na facebook.
Mutanen da abin ya shafa sun hada da tsoffin Gwamnonin jihar Ekiti biyu, Kayode Fayemi da Ayo Fayose; tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle; Gwamnonin jihar Enugu, Chimaroke Nnamani da Sullivan Chime; Tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Adamu; tsohon Gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.
Sauran sun hada da tsohon gwamnan jihar Ribas, Peter Odili; Tsohon Gwamnan jihar Abia, Theodore Orji; Tsohon Gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje; Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aliyu Wamako; Tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva; da Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.
Bello Matawalle, Wanda a halin yanzu yake rike da muƙamin Ministan tsaro a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, ana tuhumar sa da laifin karkatar da kudade N70bn; yayin da Fayemi, wanda ya rike mukamin ministan ma’adanai mai tsafta a majalisar ministocin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa na binciken Fayose, wanda ya yi wa’adi na biyu a matsayin Gwamnan jihar Ekiti, bisa zargin almundahanar N6.9bn.
Ana tuhumar Nnamani kan badakalar N5.3bn; Ana binciken Chime ne a kan badakalar Naira miliyan 450 a yakin neman zabe a wani bangare na N23bn da ake zargin Tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison-Madueke ta raba, yayin da ake binciken Abdullahi Adamu kan zargin almundahanar N15bn.
Ana tuhumar Kwakwanso bisa zargin rashin tura asusun fansho na N10bn; Ana binciken Orji kan zargin karkatar da kudi N551bn; yayin da kuma ana binciken Odili bisa zargin damfarar N100bn. Har yanzu dai ba a san yadda za a Gudanar da binciken Tsohon Gwamnan jihar Ribas ba Saboda ya samu umarnin dakatar da hukumar EFCC da sauran jami’an tsaro daga wata babbar kotun tarayya a watan Maris na 2008, wanda har ya zuwa yau ba a bar ta ba.
Hukumar ta Gurfanar da Danjuma Goje bisa zargin almundahanar N5bn; Ana binciken Wammako bisa zargin karkatar da naira Biliyan 15; Sylva, Wanda Tsohon Ƙaramin minista ne a ma’aikatar man fetur a zamanin mulkin Buhari, na fuskantar bincike kan zargin karkatar da kudade N19.2bn; yayin da ake binciken Lamido kan badakalar N1.35bn.
Ana ci gaba da binciken Diezani kan wasu zarge-zargen almundahanar kudade da suka shafi biliyoyin Naira da miliyoyin daloli.