DPO ya ƙi karɓar cin-hancin Naira miliyan 1 a hannun bandit din da ya kama


Wani DPO na ƴansanda ya ki amincewa da cin hancin naira miliyan daya da wani da ake zargin ɗan fashin jeji ne ya ba shi bayan an kama shi a wani otal da ke garin Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa dan fashin jejin da aka kama ya bayar da cin hancin daga cikin kudin fansa da ƴansanda suka kwato daga hannunsa a wani otal da ke unguwar Tafa.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda a jihar, ASP Mansir Hassan, a yau Alhamis, an kama ɗan fashin jejin ne a ranar 19 ga watan Janairu, 2024.
Daliy Nigerian hausa ta ruwaito a cewarsa, rundunar sashen ta samu sahihin bayanai cewa wanda ake zargin na zaune a otal din st Easyway a garin Tafa.
Ya bayyana cewa jami’ansu, karkashin jagorancin jami’in ƴansanda na cajiofis sun kai farmaki otal din ne suka kama wani matashi mai suna Bello Muhammad dan shekara 28 daga jihar Zamfara tare da kwato kudi Naira miliyan 2,350,000:00, wadanda ake zargin na satar mutane ne.
Ya ce a lokacin da ake gudanar da bincike, wanda ake zargin ya amince cewa shi mai garkuwa da mutane ne da ke gudanar da ayyukan sa na laifi a dajin Kagarko a Kaduna.
ASP Mansir ya ce kudin da aka ambata na hannun wanda ake zargin na kudin fansa ne da aka karba, ya kara da cewa cakin wayarsa ya tabbatar da laifin wanda ake zargin yayin da aka dauko hotunansa dauke da bindiga kirar AK47 a dajin.
~Daily Nigerian Hausa