Dalilin ci gaba da garkuwa da mutane, duk da an yi wa layukan waya rajista da lambar katin ɗan ƙasa, NIN – Isa Pantami
Za’a iya hada lambobin waya 7 da lambar katin zama dan kasa 1 – Pantami


Tsohon Ministan Sadarwa da Inganta Fasaha, Isa Pantami, ya bayyana cewa ana samun yawaitar garkuwa da mutane duk kuwa da an haɗa lambobin waya da lambar rajistar ɗan ƙasa (NIN), saboda hukumomin da suka kamata su yi aiki da tsarin, ba su yi ba sun yi watsi da shi.
Pantami ya yi wannan ƙarin haske ne yayin da ya ke maida raddi ga wata magana da Mentus ya yi, inda ya tambayi dalili ko amfanin kwana da kwanaki da mutane suka ɓata su na bin layin haɗa rajistar layi da ɗan ƙasa, amma kuma yin hakan ya kasa magance matsalar garkuwa da mutane.
Daga nan sai Pantami ya shiga cikin shafin Tiwita inda aka yi bayanin, shi kuma ya yi raddi ko ƙarin haske.
Premium Times hausa ta ruwaito cewa, dama dai kafin nan wani abokin Pantami ya tara Naira miliyan 50 matsayin gudunmawa a ƙoƙarin da wasu ke yi na su haɗa Naira miliyan 100, matsayin kuɗin fansar wasu mata shida da aka yi garkuwa da su a Abuja.
Ya ce ya yi magana da mahaifin su, bayan da ‘yan bindigar suka harbe ɗaya mai suna Najeeba, saboda mahaifin su ya yi lattin kasa kai masu Naira miliyan 60 da suka nema a biya su kafin su sako matan.
Pantami wanda shi ne ya fito da tsarin haɗa lambar waya da NIN, lokacin da ya ke Minista, ya ce matsalar rashin bin tsarin da wasu hukumomin gwamnatin tarayya suka ƙi yi ne ya haifar da kasa daƙile matsalar masu garkuwa da mutane.
“Jami’an tsaron da suka kamata su tsare rayukan jama’a ne ba su bin tsarin, shi ya sa ake ci gaba da garkuwa da mutane,” inji shi.
Pantami ya ce akwai lokacin da aka yi amfani da tsarin aka yi nasara har sau uku, lokacin da ya na Minista. Amma dai bai bayyana irin yadda aka aikin ko irin nasarar da aka samu ba.
Ya tunatar cewa har barazanar kisa an yi da ya shigo da tsarin, amma ya ce ya ƙi bada kai bori ya hau.
“Ni na fi damuwa fiye da kowa, saboda har barazanar kisa an yi min saboda na kawo tsarin. Amma na ƙi bada kai bori ya hau. Na tsaya tsayin-daka sai da aka fara amfani da tsarin.”