Da Kaina Zan Jagoranci Gurfanar da Waɗanda Ake Zargi Da Cin Hanci da Rashawa – Sabon Shugaban ICPC
Sabon Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, Dr. Musa Adamu-Aliyu (SAN), ya sanar da wani sabon salo na yaƙi da cin hanci da rashawa a yayin Ganawarsa da manema labarai a Abuja.
Dr. Aliyu yayi alkawarin da kansa zai jagoranci Gurfanar da mutanen da hukumar ICPC ke tuhuma da aikata almundahana.


Yasha alwashin shiga cikin Kotuna da kuma taka rawar Gani a shari’o’in, Tare da Tabbatar da bin hanyar da ta dace don cika aikin hukumar. “Ina da Burin kasancewa a shari’ar da ICPC ta fara a matsayin mai Gabatar da kara, Tare da nuna jajircewarmu Wajen Ganin mun Hukunta masu cin hanci da Rashawa,” inji shi
Yunƙurin Dokta Aliyu na kawo sauyi ya kuma haɗa da baiwa manyan lauyoyi da ke cikin hukumar damar Gudanar da shari’o’i yadda ya kamata. Duk da haka, matsayar da ya dauka kan shigar da kara kai tsaye a cikin muhimman tuhume-tuhume ya nuna Gagarumin sauyi a Shugabancin ICPC, inda ya kafa misali da ke nuni da tsayawa tsayin daka kan cin hanci da rashawa.