Labarai

Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da ceto mutane 35 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

Advertisment

Rundunar sojin Najeriya a jihar Katsina sun ceto mutane 35 daga hannun ƴan bindiga waɗanda aka sace garin Tashar Nagulle da ke ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina.

Katsina Reporters ta samu cewa, Sojojin sun fatattaki maboyar yan bindigar ne bayan samun bayanan sirri inda suka tarwatsa maboyar ƴan bindigar tare da kubutar mutanen da suke tsare da su ɓoye a cikin ɗakuna.Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da ceto mutane 35 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

Daga cikin mutanen da sojojin suka kubutar aƙwai matan aure da maza da ƙananan yara wanda suka ce dawa ce kaɗai abincin da ake basu a kowace rana, kamar yadda Alfijir Radio suka ruwaito.Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da ceto mutane 35 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

A makon da ya gabata ne, tun a ranar Lahadi 21 ga watan Janairu 2024. ƴan bindigar suka wani hari a kauyen Tashar Nagulle inda suka yi garkuwa da mutum 35 zuwa daji kuma suka bukaci a basu Naira miliyan 60 a matsayin kudin fansa.

Shugaban ƙaramar hukumar Batsari Alhaji Yusuf Mamman Ifo, shi ne ya tabbatar da kubutar da mutanen 35 da sojojin suka yi inda ya ce ana duba lafiyarsu kafin daga bisani a maida su ga iyalansu.Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sojoji sun tarwatsa sansanin ƴan bindiga tare da ceto mutane 35 da suka yi garkuwa da su a jihar Katsina

Har kawo wa yanzu dai rundunar sojojin ba ta yi wani karin bayani akan bukatar da mutanen ko kashe wasu daga cikin ƴan bindigar ba.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button