Labarai

Bola Tinubu ya bukaci jagororin Jam’iyyar Apc suyi sulhu da Kwankwaso

Advertisment

Bayan yanke hukuncin kotun koli da ankayi a satin da ya gabata shugaban kasa bola Ahmed Tinubu da su sasanta tsakaninsu da jagoran tafiyar darikar kwankwasiyya Dr.Engr. Rabiu Musa Kwankwaso da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Dr.Abdullahi Umar Ganduje masu sha’awar shigowa jam’iyyar APC kamar yadda munka samu rahoto ta wani dan jarida a shafinsa Ahamed Tijjani Ramalan na wallafa.

Bola Tinubu ya bukaci jagororin Jam'iyyar Apc suyi sulhu da Kwankwaso
Bola Tinubu ya bukaci jagororin Jam’iyyar Apc suyi sulhu da Kwankwaso

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da ya sasanta da Kwankwaso da duk wasu mutanen da ke shirin shiga jam’iyyar.

“Shugaban ya yi wannan kiran ne a wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na Kano, kwanaki kadan bayan hukuncin kotun koli da ya tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Shugaban ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a Kano da su bi hanyar tattaunawa da daidaikun jama’a, kungiyoyi ko jam’iyyun siyasa da suka shirya shiga jam’iyyar APC domin bunkasa hadin kai da cigaban jihar.

Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da matasan jam’iyyar APC a Kano suka roki shugaban kasa Tinubu ya sauke Ganduje daga shugabancin jam’iyyar na kasa.

Shin ta yaya kuke ganin sulhu tsakanin Kwankwaso da Ganduje zai yuwu”

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button