Birnin Lagos ya zarta biranen Dubai da Miami na Amurka Kyau a duniya
Birnin Lagos ya zarta Dubai na hadaddiyar daular Larabawa da birnin Miami na Amurka kyau a duniya.
Kamar yadda wata mujalla da ke sanya idanu kan kyawun birane a duniya mai suna Time out ta wallafa, ta ce birnin Lagos na Najeriya shine na 19 cikin jerin birane mafiya kyau a duniya.
Dclhausa na ruwaito cewa, biranen Lagos, da Cape town na Africa ta Kudu da kuma Accra na Ghana su kadai ne suka shiga cikin jerin a kasashen Africa.
Mujallar na amfani da ma’aunin dadin abinci da arhar sa, al’adun gargajiya, ababen more rayuwa, yanayin tsaro, mu’amala, guraren tarihi da sauran su wajen tantance burunkasar birni.
Wani Labari: In za’ayi gini sau dubu a masallacin Idi ko makaranta sai mun ruguje shi -Kwankwaso
Jagoron darikar kwankwasiyya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi wani takaitaccen bayyani akan rushe rushe da sunkayi a cikin jihar kano wanda abun ya ɗaga hankalin mutane irin ganin yadda ankayi asarar dukiya mai yawa.
Mu abinda munka dauka dai-dai da yawan mutane basu dauke shi dai-dai ba, kuma abinda munka dauka ba dai-dai ba dai-dai da yawan mutane sunka dauka dai-dai, kuma abinda zaka fahimta a nan shine a siyasa abubuwan da ake yi shine dai-dai da kawo cigaba, idan ba dai-dai kake yi ba, ai zaka ga babba matsala ai yanzu da suke ta jawo Abuja suje gari kaza an rushe kaza an waye masallaci.