Bayan labarin DAILY NIGERIAN, gwamnatin Nijeriya ta dakatar da karɓar kwalin digiri daga Togo da Benin


Gwamnatin ta sanar da tantance kwallon digiri da aka samo shi daga Jamhuriyar Benin da Togo tun bayan da jaridar DAILY NIGERIAN wanda ta yi akan yadda ake samun kwalin digiri cikin sauri da sauki.
A rahoton, wanda aka buga shi a ranar 30 ga watan Disamba, ya nuna yadda jami’an gwamnati suke bada hadin kai wajen badakala da cuwa-cuwar kwallon digiri din.


Wani wakilin DAILY NIGERIAN ne ya bankado bafakalar bayan da ya samu kwallon digiri a cikin sati shida ba tare da ya haura bida ya je makarantar ba.
A wata sanarwa da Augustina Obilor-Duru ta fitar a madadin daraktan yada labarai na Ma’aikatar Ilimi, gwamnatin ta nuna takaicin yadda wasu suka ɓullo da wasu hanyoyi na samun satifiket ta barauniyar hanya.
Sanarwar ta ce za a cigaba da dakatar da tantancewar har sai an kammala bincike na sirri a Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje da ta Ilimi da Ƴansandan Farin kaya da kuma hukumar NYSC a Nijeriya.
Ta ce tuni an kafa kwamiti domin fara binciken yadda lamarin ke faruwa.
Sanarwar ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su baiwa kwamitin hadin kai a yayin binciken.