Asia cup 2023: Falasdinu ta kai matakin ƴan 16 a Gasar Asian Cup


Keftin din kungiyar kwallon kafa ta Falasdinu Musab Al-Battat ya bayyana cewa kungiyarsa ta “cika alkawarin da ta dauka ga Falasdinawa” bayan ta kai zagayen sili-daya-kwale a Gasar Cin Kofin Nahiyar Asia a karon farko.
Wasan wanda aka tashi 3-0 wanda suka buga da Hong Kong a ranar Talata shi ne wasa na farko da suka fara ci a gasar kuma ya kai su matakin ƴan 16 a matsayin daya daga cikin huɗu mafi kyau.
Oday Dabbagh shi ne ya kasance gwarzo a Doha inda ya zura kwallaye biyu, sai kuma a usur ɗin ƙarshe da aka busa, sai ƴan wasan Falasdunawa da ma’aikata suka rinƙa mutrna a fili tare da runugmar juna da ɗaga tutoci.


Jaridar TRT Afrika hausa sun ruwaito cewa, haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta zo ta biyu a rukunin C duk da cewa ta yi rashin nasara a ci 2-1 a Iran.
Nasarar da Falasdinu ta samu a kwallon kafa na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai mata hare-hare da kuma yin ƙawanya a Gaza.
Ƴan wasa da ma’aikata sun rasa masoyansu sakamakon hare-haren Isra’ila. “Ina so na gode wa duk wadanda suka ba mu goyon baya, “in ji shi.
“Mun yi nasarar sanya murmushi a fuskokin wadanda ke bin mu … ciki ko wajen Falasdinu. Kafin a soma wasan, an yi ta yin ihun “a ba Falasdinawa ‘yanci”.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





