An ƙaddamar da Littafi a kan yadda Buhari ya mulki Najeriya


Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya halarci taron bikin ƙaddamar da wani littafin mai suna “Work With Buhari” a ɗakin taro na Congress Hall of Transcorp Hilton Hotel da ke Abuja,
Katsina Reporters ta samu cewa, littafin wanda tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa Femi Adesina, ya rubuta kan yadda tsohon shugaban ƙasar ya mulki Najeriya tare da gabatar da mujalladi biyar na wani littafi mai suna ‘Muhammadu Buhari, The Nigerian Legacy, 2015 to 2023’.
Taron mai ban sha’awa wanda ya samu halartar shugaban Najeriya Bola Tinubu, da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji Yakubu Gowon da shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.
Wannan ita ce ziyara ta farko da Buhari, ya kai a birnin tarayya Abuja tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 da ya mika wa Tinubu shugabancin Najeriya.
Wani labari : Al’umma sun fara gudun Hijira zuwa wasu garuruwan saboda matsalar tsaro a jihar Katsina
Al’ummar ƙauyen Nahuta da ke garin Batsari a jihar Katsina na cigaba da yin gudun Hijira zuwa wasu garuruwan sakamakon yawaitar haren haren ƴan bindiga da mutanen yankin suke fuskanta na kashe kashe da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa.
Al’ummar sun fara yin gudun Hijirar ne tun bayan da ƴan bindigar suka kai hari a wani sansanin sojoji a garin Nahuta a daren ranar Asabar, inda suka ƙona motocin soji 2 suka ɓalle shaguna suka ƙwashi abinci da dabbobi suka yi awon gaba dasu zuwa daji.
Wanda hakan ya janyo al’ummar garin maza da mata da ƙananan yara suke cigaba da barin gidajensu tare da ƙwashe kayayyakinsu suna barin garin domin gudun ceton rai.
A zantawar da muka yi da wani mazaunin yankin ya shaida ma Katsina Reporters cewa mutanen da suka yi gudun Hijirar suna tafiya gidan sarkin Ruma a Batsari wasu na tafiya cikin birnin Katsina.