Labarai

Yunwa da kishirwa na yi wa Falasdinawa 500,000 barazana

Hare-haren da Isra’ila ta kwashe sama da wata biyu tana kaiwa a Gaza sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa fiye da 17,487, galibinsu mata da kananan yara sannan fiye da mutum 46,480 sun jikkata.

Falasdinawa dubu 500 ke cikin barazanar yunwa da kishirwa a biranen da hare-haren Isra’ila ke kara karuwa, kamar yadda gwamnatin Gaza ta bayyana.

Jaridar trtafrika na ruwaito Gwamnatin ta Gaza ta ce jama’ar birnin na cikin bala’i sakamakon dagangan Isra’ila ke kai hare-hare kan ababen more rayuwa da ke da alaka da abinci da ruwa.

Mai magana da yawun birnin, Hosni Muhanna ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a ranar Asabar cewa karancin man fetur yana kawo cikas wurin kwasar wadanda suka samu rauni da kuma jigilar gawawwaki.

Yunwa da kishirwa na yi wa Falasdinawa 500,000 barazana
Yunwa da kishirwa na yi wa Falasdinawa 500,000 barazana

Isra’ila na ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza bayan Amurka ta ki amincewa da kudurin

Isra’ila ta ci gaba da zafafa kai hare-hare a Gaza bayan Amurka ta yi fatali da kudurin da aka gabatar ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda zai bayar da dama a tsagaita wuta a hare-haren da Isra’ila take kaiwa Gaza.

Hamas da hukumomin Falasdinu sun yi Allah wadai da wannan matakin na Amurka a daidai lokacin da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa mutum 17,487 suka mutu a Gaza, akasari mata da yara.

Haka kuma wani hari da Isra’ila ta kai a kudancin birnin Khan Yunis ya kashe mutum shida, inda wasu biyar suka mutu a wani hari na daban a Rafah, kamar yadda ma’aikatar ta tabbatar a ranar Asabar.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button