‘Ya’yana 4 amma har yanzu maza rububina suke – Sandra Iheuwa


Yanzu hak ni mahaifiyar ‘Ya ‘ya hu’du 4 ce amma Ina shagalina Kuma hamshakan attajirai har yanzu suna marari na.
Shahararriyar ‘yar kasuwa, Sandra Iheuwa ta bayyana cewa duk da kasancewarta uwar ‘ya’ya 4, attajirai na ci gaba da bibiyar ta, duk da cewa tana ba da shawara ga mata masu aure.
Ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Asabar yayin da take yabawa kanta sosai tare da yin kira ga sauran mata masu aure a fadin duniya da kada su bari matsayinsu ya takaita su.
Ta rubuta, “Ni mahaifiyar ‘ya’ya 4 ce…. maza suna rudewa a kaina ba kawai maza ba biloniyoyi nake nufi…
“A matsayin uwa daya tilo, kada ku iyakance kanku, kuyi abu mafi kyau kuma ku kasance mafi kyawu, Tabbas abubuwa masu kyau zasu fado a gare Ku.
Wani labari : KAJI RABO: Daga Zuwa Gaisuwa, An Yi Musu Aure Nan Take a cikin hotuna
Wata budurwa mai suna Majida Muhammad ta bayyana cewa an ɗaura aurensu bayan Masoyinta ya je gaisuwa da saka ranar aure a gidansu. Kamar yadda ta bayyana a shafinta na facebook.
“Daga gaisuwa da saka rana ya rikiɗa ya zama ɗaurin. Don Allah ku sanya mana albarka.
Ƴan’uwa ku taya mu addu’a Allah ya sa mana albarka a wannan aure, Ya zaunar da mu lafiya, Ya kauda mana dukkanin abin ƙi, ameen.
Officially Mrs Muhammad Nasir Jajere. AlhamdulilLah. – inji majida Muhammad.