Labarai

Yawan matalauta ya ƙaru zuwa miliyan 104 a Najeriya – Bankin Duniya

Advertisment

Wani rahoto na Bankin Duniya, ya bayyana cewa yawan mutanen da ke cikin ƙangin talauci a Najeriya ya ƙaru, daga kashi 40% a 2018 zuwa kashi 46% a 2023.

Wannan na cikin abubuwan da ke ƙunshe a sabon rahoton, wanda babban jami’in bankin mai kula da tattalin arziƙi a Najeriya, Alex Sienaert ya gabatar a lokacin fitar da rahoto a kan ci gaban Najeriya cikin 2023, a Abuja.
Sai dai rahoton ya ce sauye-sauyen da gwamnatin ƙasar ta kawo, za su iya rage yawan mutanen da ke faɗawa cikin talauci a shekaru masu zuwa, ko da yake abin zai ɗauki lokaci.
Amma a yanzu, rahoton ya ce hauhawar farashi na kayan masarufi da tafiyar hawainiya a lamarin ci gaban ƙasar, na ci gaba da ingiza mutane cikin talauci.

Lamarin da ya sanya aka samu ƙarin mutum miliyan 24 da suka faɗa ƙangin talauci a tsakanin shekarar 2018 zuwa 2023.
Rahoton ya ce a 2018 yawan mutanen da ke fama da talauci, ya tsaya ne a kan miliyan 79, amma a 2023 yawan ya kai miliyan 104.jaridar liberty Tvr na ruwaito

Yawan matalauta ya ƙaru zuwa miliyan 104 a Najeriya - Bankin Duniya
Yawan matalauta ya ƙaru zuwa miliyan 104 a Najeriya – Bankin Duniya

A cikin biranen Najeriya, yawan talakawa ya ƙaru daga miliyan 13 zuwa miliyan 20, yayin da matalauta a yankunan karkara, ya ƙaru daga miliyan 67 zuwa miliyan 84.
Shawarwarin da Bankin Duniya ya bai wa Najeriya
Al’ummar Najeriya sun shiga cikin halin matsin rayuwa sanadin wasu manufofi da gwamnatin Najeriya ta ɓullo da su.
Ciki akwai cire tallafin man fetur da sauya tsarin harkokin kuɗi.
Waɗannan abubuwa sun haifar da rashin tabbas da kuma tsadar abinci da na kayan masarufi.

A sabon rahoton nasa, Bankin Duniya ya ce duk da yake gwamnatin Najeriyar na ɗaukar matakan tallafa wa al’umma, akwai buƙatar ɓullo da ƙarin wasu matakai, waɗanda ta hanyarsu ne tattalin arziƙin ƙasar, zai farfaɗo kuma ya ɗora Najeriya a turbar ci gaba.
Cire tallafin man fetur gaba ɗaya

A ranar 29 ga watan Mayu ne, shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur.
Duk da cewa gwamnati ta ce ta tara kuɗaɗe da suka kai kimanin tirliyan biyu a 2023, saboda dakatar da biyan tallafin mai, matakin ya sauya lamurra a ƙasar ta Najeriya.
Farashin man fetur ya nunka sau uku, kuɗin sufuri ya yi tashin gwauron zabi sannan farashin kayan masarufi sun ɗaga sosai.
Rahoton na Bankin Duniya ya ce kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta tabbatar da ƙudurin nata na cire tallafin mai.
Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin cewa gwamnatin na ci gaba da biyan wani kaso tallafin man fetur ɗin a kaikaice.
Rahoton ya bayyana cewa farashin man fetur da ake da shi a yanzu, bai yi daidai da ainihin yadda farashin ya kamata ya kasance ba.
Haɗe kasuwar musayar kuɗi
Tun a watan Mayu, darajar naira ta faɗi da kimanin kashi 40%, in ji rahoton na Bankin Duniya.
Hakan ya faru ne sanadin sauye-sauye a fannin kuɗi na ƙasar.
Babban Bankin Najeriya ya ayyana haɗe kasuwar musayar kuɗi tare da barin kasuwa ta yi halinta game da darajar naira.
Gwamnatin da ta gabata ta ƙayyade farashin naira, sai dai hakan ya haifar da bambanci mai yawa tsakanin darajar naira a hukumance, da kuma darajarta a kasuwannin musayar kuɗi na bayan fage.

Bankin Duniya ya ce wajibi ne Najeriya ta tabbatar an aiwatar da wannan tsari domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar.

Ƙara haraji

Tun a shekarar 2019 ne gwamnatin Najeriya ta fito da wasu tsare-tsare wajen faɗaɗa hanyoyin kuɗaɗen shiga baya ga man fetur.
Wasu daga cikin matakan da gwamnati ta ɗauka sun haɗa da ƙara harajin da ake karɓa wajen al’umma.
Rahoton bankin na duniya ya ce ya kamata gwamnatin ta ƙara harajin da ake karɓa a hannun al’umma.
Haka kuma, kamata ya yi a cire afuwar biyan haraji ga abubuwan da ake samarwa daga ɗanyen mai.

A riƙa karaɓar haraji kan harkokin sadarwa, da robobi, da kuma motoci masu yawan guraɓata muhalli.

Soke haramcin shigo da kaya

A watan Oktoba ne, Babban Bankin Najeriya ya soke haramcin bayar da canjin kuɗi kan shigo da kaya 43 daga ƙasashen ƙetare.
Ana sa ran hakan zai saukar da farashin kayan abinci kamar shinkafa da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga.
Bankin duniyan ya ce ya kamata a sassauta kuɗin fiton shigo da kaya daga ƙasashen waje da kuma cire haramcin shigo da kayan abinci da magunguna.
A cewar bankin “dokokin da aka sanya a baya na haramcin shigo da kaya daga waje ba su cimma manufar samar da su ba.”

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button