Labarai

Yawan amfani da wayar salula na sa karancin maniyyi a jikin Dan’adam – Binciken masana

Yawan amfani da wayar salula na taimakawa wajen kawo karancin ruwan maniyyi a jikin Dan’adam kamar yadda binciken masana a kasar Switzerland ya gano.

Binciken ya gano cewa matasa maza masu shekaru 18-22 da ke amfani da wayar salula sau 20 a rana, na a sahun gaba wajen haduwa da wannan hatsarin na karancin ruwan maniyyi.

Wani labari :Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jiha.

Nadin ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala Mni ya yi na radin kansa wanda gwamnatin yanzu ta rike tun daga kafuwarta a watan Mayu, 2023.

Alhaji Abdullahi Musa Kwararren ma’aikacin gwamnati ne wanda ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi daban-daban a Kano sama da shekaru talatin, ya fito ne daga karamar hukumar Kiru.

Gwamna Abba Kabir ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan jihar da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a cikin dokokin da suka shafi aikin gwamnati.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button