Yaudara ko ganganci : Matashi dan shekara 17 ya ɗirkawa bazawara ƴar 31 ciki a Kaduna
A yammacin jiya ne aka Kama wata bazawara da kai yara bayan kango don suyi amfani da ita ta biya su, kamar yadda jaridar alfijir hausa Majiyar ta ke shaida mata haka.
An dai Kama matar ce da bai san an baiyana sunan ta ba ‘yar Asalin hayin rigasa dake garin Kaduna alokacin da aka ganta ta shiga da wasu yara matasa bayan kango ɗin don gudanar da abinda suka saba.”
Sai dai ita wannan mata taso tayi gardama alokacin da aka cika hannu da ita, sai dai ta faɗi gaskiyan abin da ya sa ta ke baiwa ƙananan dama su yi lalata da ita.
Da ALFIJIR ta tuntube ta don jin dalilin da yasa baza tayi aure ba kawai ta huta? sai ta ce mazan ne ma yaudara, domin a cikin maneman nata da yawa kowa yazo sai dai ya neme ta da fasikanci idan an ce ya fito sai anemeshi a rasa Kamar walkiya.
Bugu da kari hukuma ta nemi da lallai ayi gwaji a wurin masana lafiya akan ita bazawarar dan gudun shafawa kananan yaran wani cuta daban, bayan da aka kaddamar da bincike na gwaji aka gano cewa; ta na dauke da juna biyu, ta Bayyana cewa; wani matashi ne wanda mai wuce shekara 17 ba ta san sun dade suna goge raini ya yi mata wannan ta’asar.”